Dan gaye
Yai ado da ganye
Ga shi kamar ya waye
Amma kwanya ta juye
Wajen laluben Hauro a tsaye
An jinka wa wasu kayan maye
A jinka musu ladar tawaye
La’adar alaye
An maishe su dolaye
Suna ahayye nanaye
Miyagu na ta kewaye-kewaye
Gayu na ta zagaye-zagaye
Da kudi ake muku kaye
Ko’ina sun mamaye
Sun sayi kuri’a sun boye
Tsautsayin tsaye-tsaye
Tsilla-tsillar tusuntsaye
Tsamin tsamiyar tsinkaye
Tanderun tandar toye-toye
Takurar takun tagwaye
Cinikin kuri’u
Ya rudar da mutane
Batu ne sananne
A bar batun wane da wane
Mummuna a kawar lu’u-lu’u
Ranar sili da zagaye
Mummunar ta’ada ta zuganye
Illolinta an yaye
Masana sun yi kiranye
Sun ce mu daina jaye-jaye
Watan Noman-Baba
Takatsantan da romon jaba
Bikin dare guda an caba
tunkarar juna da wuka a daba
Mui wa mutunci haba-haba
Shekarar silin madambaci
An hana ha’inci
A kiyayi yi wa juna habaici
Cinikin kudi ya baci
Dabarbarun jefa al’umma a kunci
Babban Bakin Ce-ce-ku-ce
Tsaba da tsakuwa a tantance
Bambamin bambance-bambance
matsabbai sun sa an susuce
wayar da ka ne a fakaice
A ranar sili da zagaye ga watan Noma-Baba na shekarar dubu karamin lauje da sili da madambaci, BAMBAMIN BATUTUWAN BABBAN BAKIN CE-CE-KUCEN Lantsandan ya shirya shirin ankararwa kan munin cinikin kuri’u, al’amarin da suka yi nuni da cewa zai iya haifar da zazzabin zabuka a shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa da ke karatowa. Illa dai mafi muni ita ce, cefanar da kasa ga jigari-jigarin jagoran jan ragamar rugurguza zamantakewa da tattali da siyasa.
Dimbin masana daga jam’in jama’ar jami’ar Mai martaba na Birnin Dabo suka halarci wannan gangami, inda suka nusar da al’umma muhimmancin bin doka. Sannan masu fafutikar damo-da-kura-da-diyya a karkashin tutocin jam’iyyun dan boto da sanda jirge, da tsintsiyar kwakwa da ta laushi ba tare da tsiya-tsiya ba, sun hallara, inda suka nusar da gama-garin mutane yadda ya dace a kada kuri’u.Kuma wani tsohon dan NEHU, dattijon da ya san Aminin siyasar Kanawan Dabo, wato AbdulKarimu Dayyabu ya tabbatar da cewa Malam Nagidan Mambayya ya hana karbar NA-AHU, musamman a wajen takarar zaben wanda duk zai bai wa al’umma kyakkyawan wakilci, don zama ja-gaban jan ragamar jagoranci managarci.
Kodayake dai wani garjejen gaye, wanda ya yi nuni da cewa kansa ya waye daidai lokacin da gari ya waye, a da ana ba su ’yan matsabbai, su bi farfajiyar gidajen al’umma su nunke su a baibai.
Irin wannan tabargaza ta cinikiyyar masu kada kuri’u a kakar kasurarta, Malam Na-kwaciri ya bayyana mana cewa, masu fuka-fukin tashi a birnin Dabo, har GWANJON GWANGWAJEWAR GANYEN GAYE suke yi, domin wanda duk ke da muradi sai ya taya, in aka sallama shi ke nan an yi GA WURI, GA WAINA . Sai dai wani hanzari ba rarewa a guje ba, masanan da Babban- Bakin Ce-ce-ku-ce ya gayyato sun tabbatar wa mahalarta taron cewa,’ LADA DA LA’ADAR LODIN LAFTUN LALLAGA LUMANA,’ ake auno wa al’umma. Kuma kin amincewa da faruwar GWANJON GWANGWAJEWAR GANYEN GAYE, tamkar inkarin ikrari kan maganar tsari, wato ga waina, ga wuri, inda rashin wuri ke rusa jari ga zuki-ta-malle iri-iri.
Haurobiyawa dai sun saba da walle-wallen wasan Samson-siya-siya da kwakwalwar talakawa da ’yan takara da masu taka karan danni ke tsuwurwurtawa. Domin tsawon mulkin mulaka’u na jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, wanda aka shafe shekaru sili da manuniyar sama ana fama, ba wani abin ta’ajibi ba ne a hango wadanda suka yi ado da ganyayyaki a kan layin kada kuri’a. Shi ya sa ma nake ganin magabtan al’umma sun yunkuro da ’yan matsabbai don su nunke jama’a a baibai.
’Yan makarantar Dodorido da ke koyon falle shafukan mujallu da makalu da wagagen litattafai a farfajiyar wannan makaranta da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, lokaci ya yi da za mu tabbatar da batun Malam Mai yaren Hauhau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, cewa: Halin mutum jarinsa.” Lallai mu yi karatun ta-natsu, don gudun kada a karke da tsilla-tsillar tsallen badake kamar tsuntsu, wanda kwanyarsa ta motsu. ’Yan makaranta mu natsu, mu daina yi wa juna nunin yatsu, mu himmatu ka’in da na’in wajen ganin kyawawan ta’adu sun hau tudu sun warwatsu.
A nan ya kamata mu fasko cewa duk wanda ke fargabar cafke SAMARIN KUSU DA ’YAN MATAN JABA DA GAFIYA, to shi ne ke kwakwar kundunbalar kundume kuri’u, sannan jama’ar da hankalinsu yake a hannun taguwa, su ne ke cancancarewa a carin ’ Gwanjon gwangwajewar ganyen gaye.’
Bisa la’kari da shirin da magabta al’umma ke yi na cinikin RA’AYI, don su mayar da shi RAIRAYI, manhajar makarantarmu mara hajijiya za ta ci gaba da baje dabarun bin DOKA don kada kowa ya KOKA, tare da kawar da JUHALA don tabbtar da ADALA, ta yadda daukaci al’umma za su ji dadin yin WALWALA, tare da karsashin rashin KASALA a duk lokacin da suka yi bitar MAKALA, ta yadda cikin sauki za a fasko cewa ba ma TALLA. Kuma wadanda ke cinikin ALALA su ne ke laluben GALALA don dinka galleliyar GALILA, ta yadda za su ji dadin sanya gama-garinal’umma su yi tadundume kururu da GAJALA.