✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnoni kan ki gudanar da zakukkukan kananan hukumomi don su…

A taron hadin guiwa da aka gudanar a cikin makon da ya gabata a Kaduna tsakanin Hukumar Zake (INEC) da Hukumomin Zake na jihohi, daya…

A taron hadin guiwa da aka gudanar a cikin makon da ya gabata a Kaduna tsakanin Hukumar Zake (INEC) da Hukumomin Zake na jihohi, daya daga cikin batutuwan da sanarwar bayan taron ta yi tsokaci a kai shi ne lallai gwamnonin jihohi 11 da ya zuwa yanzu ba su da zakakkun shugabanni da kansiloli a majalisun kananan hukumomin jihohinsu, su gaggauta yin hakan, ta yadda za a tabbatar da mulkin dimokuradiyya tun daga tushe. Wadannan jihohin su ne na Katsina da Delta da Ekiti da Barno da Osun da Kano da Oyo da Abia da Bauchi da Imo da Ondo.
Taron, sun ce sun kira shi ne khususan ta yadda hukumomin za su duba yadda suke gudanar da ayyukansu na zakukkuka a kasar da aniyar su iya duba matsaloli da kura-kuran da sukan fuskanta da aniyar yadda za su gyara su, musamman bisa ga tunkarowar zakukkukan kasa na shekara mai zuwa, in Allah Ya nuna mana. Hukumar INEC dai, ita ke da alhakin gudanar da zakukkukan kasa irin na shugaban kasa da na gwamnoni da na `yan Majalisun Dokoki na kasa da na jihohi, yayin da hukumomin zake na jihohi ke da alhakin gudanar da zakukkukan shugabanni da kansilolin kananan hukumomi.
Mahalarta taron sun nuna damuwarsu a kan yadda a jihohi 10, kwamitocin riko ake da su da suke tafiyar da al`amurran yau da kullum na kananan hukumominsu. karewa ma a jihar Delta ko kwamitocin rikon gwamnati ba ta iya nadawa ba, sai kawai ta bar harkokin gudanar da majalisun kananan hukumomin a hannun daraktocin mulki. Wannan tsari ko kusa, inji hukumomin zaken, ba ya taimaka wa harkokin gudanar da mulkin dimokuradiyya tun daga tushe, alhali tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa na 1999 da aka yi wa kwaskwarima sun tanadi samar da majalisun kananan hukumomi masu zakakkun shugabanni da kansiloli.
Ra`ayin Hukumomin zaken biyu ne, na lallai akwai bukatar gwamnatocin jihohi su rika ba Hukumomin Zakensu `yancin cin gashin kai, ta fannin kudade da wadatuwar kayayyakin aiki, don a fadarsu ta haka ne kawai, Hukumomin zaken na jihohi za su iya gudanar da zakukkukan kananan hukumomi cikin inganci da kwarewar da take ita ce. Sun kuma nemi jam`iyyun siyasa su dukafa wajen wayar da kawunan magoya bayansu a kan harkokin zake, lamarin da zai taimaka wa harkokin gudanar da mulkin dimokuradiyya. Makasudin shirya taron dai, inji Hukumar INEC, shi ne yadda za su iya tattauna matsalolin gudanar da zakukkuka tsakanin hukumomin biyu.
Wannan taro ya tunatar da ni irin koke-koken da ake ta fama da su a kan hukumomin zake na jihohi, wadanda akan kira “Ka ci, ba ka ci ba, ka ci”. Ma`ana, bisa ga yadda hukumomin suka yi kaurin suna a kan dukkan jam`iyyar da ke kan karagar mulki a jiha, ita take lashe dukkan kujerun da aka yi takara a kansu, kama daga shugabanni da kansilolin dukkan majalisun kananan hukumomin da ke jihar, al`amarin da ya kai matsayin da ko da kansila daya ba ka jin wata jam`iyyar adawa ta ci a jihar.  
Irin wannan tsari na cinye duk, ya sanya aka dade ana ta kiraye-kirayen lallai sai a dauke ikon gudanar da zakukkukan majalisun kananan hukumomi daga hannun hukumomin zake na jihohi a mayar da su hannan Hukumar zake ta INEC. Ko a karshen shekarar 2012 da Majalisun Dokoki na kasa suka gudanar da jin ra`ayoyin jama`a a kan gyaran kundin tsarin mulkin kasar nan, wannan batu na cikin batutuwan da suke kan gaba a bakunan jama`a, na sai a duba.
Kodayake, ba gwamnonin jihohi suka tanadarwa kansu ikon mallake hukumomin zakensu na jihohi, bare kuma ikon guudanar da zakukkuka ko kuma nada kwamitocin riko inda ba a yi zake ba, tanade-tanaden kundin tsarin mulki ya tanadar masu da haka, amma kuma ya ci a ce gwamnonin jihohin suna koyi da Hukumar zake ta INEC, wadda shugaban kasa bai taka hawa kujerar naki a kanta ba, bare ya hana ta gudanar da zake inda duk bukatar hakan ta samu.
Su ma gwamnonin jihohi sukan yi haka ne saboda kawai kwadayin su rika mallake kudaden shigar majalisun kananan hukumominsu, al`amarin da muninsa ya kai ko da inda aka yi zake a majalisun, za ka taras ta ajiyar nan ta hadin guiwa da ake da ita tsakanin gwamnatocin jihohi da majalisun kananan hukumominsu, sai abin da gwamnonin suka ga dama suka ba majalisun, alhali tanadin cewa ya yi su hada wancan asusu kawai a kudaden shiga na cikin gida da suka tara, sannan su raba, amma ta kai hatta kudaden shigarsu daga asusun gwamnatin tarayya suke handamewa. Wannan ya kai matsayin akasarin wasu ayyukan raya kasa da wasu gwamnatocin jihohi suke yi da kudaden majalisun kananan hukumominsu da suka rike suke gudanar da su.
A tsari na wannan mulkin dimokuradiyyar da muke ciki yau shekaru 15, tanade-tanaden da ake da su a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan, sun tanadi gwamantoci uku na kasar nan, kowace ta ci gashin kansa (gwamnatin taraya da gwamnatocin jihohi da kuma majalisun kananan hukumomi) kusan a kan komai, amma a lokacin da gwamnatin tarayya take sakar wa gwamnatocin jihohi mara suke fitsari yadda suke so wajen sarrafa kudadensu, majalisun kananan hukumomi ba su da gatan haka.
A tafiyar tsarin mulkin da ake ciki, ya ci  a ce majalisun kananan hukumomin suna da kwararrun ma`aikata irin su likitoci da injinoyi da akantoci da makamantan ma`aikata, don ciyar da majalisun gaba, amma ina! Har yanzu babu irin wadannan ma`aikata, inda kuma ake da su za ka taras ba su aikinsu yadda ya kamata. A takaicen takaitawa majalisun kananan hukumomi a kasar nan kara zube suke, kai ka ce ba gwamnatoci ba ne. Ina ga lokaci ya yi a wannan karon kungiyar Ma`aikatun kananan Hukumomi da sauran kungiyoyin kwadago da na kare hakokin bil Adama, su mike tsaye su yi duk abin da za su iya wajen ganin sun ceto majalisun kananan hukumomin kasar nan daga hannun gwamnonin jihohi.