Gwamnatin Tarayya ta sanar da ƙudirinta na kirkiro Hukumar Kula da Filaye ta Kasa.
Ministan Gidaje da Tsara Birane, Ahmed Dangari ne ya bayyana hakan, a taron zuba jari na ’yan Nijeriya mazauna kasashen ketare, karo na 6 da ya gudana a Abuja.
- Ana zargin matar aure da kashe mijinta da taɓarya a Gombe
- An ba hammata iska tsakanin ’yan sanda da jami’an shige da fice a Maiduguri
Ministan ya ce samar da sabuwar hukumar zai taimaka wajen kula da hakkin mallakar filaye a kasar nan.
Dangari ya kuma ce kirkiro hukumar na daga cikin sabbin manufofin Gwamnatin Tinubu na saita hanyoyin mallakar filaye.
“Rahoton kwamitin da shugaban kasa ya kafa kwanakin baya ya samar, kan sabbin dokokin mallakar filaye, karkashin Farfesa Peter Adeniyi, za a yi amfani da shi a sabuwar hukumar.
“Babu wata kasa da za ta samu ci gaba, ba tare da ta inganta dokokin kula da filayenta ba, ”in ji Dangari.