✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa kananan manoma da taraktoci 600 a Jihar Adamawa

Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa kananan manoma da taraktoci 600 a karkashin shirinta na ‘Anchor Borrowers’ a Jihar Adamawa, musamman yankunann da suka fuskancin tsananin…

Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa kananan manoma da taraktoci 600 a karkashin shirinta na ‘Anchor Borrowers’ a Jihar Adamawa, musamman yankunann da suka fuskancin tsananin rayuwa sakamakon rikicin Boko Haram.

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya nuna farin cikinsa da godiya bisa wannan tallafi da Gwamnatin Tarayya ta kawo jiharsa domin tallafa wa kananan manoman.

Gwamnan ya kara da cewa wannan irin tsarin da Gwamnatin Tarayya ta kawo zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki a yankunan da suka fuskanci kalubale a lokacin da rikicin Boko Haram ya yi tsanani.

Ya ce zai iya iya kokarinsa domin ganin cewa wadannan yanukuna sun samu taraktocin don ci gaban Jihar Adamawa ta wajen gudanar da ayyukan noma, wanda hakan zai samar da ayyukan yi ga al’ummar jihar baki daya.

Shugaban Kungiyar Ilimantarwa da Kare Harkokin Noma ta Kasa (NECAS), Sadik Umar Daware a yayin da yake jawabinsa ya ce kasancewar Jihar Adamawa ta fi yawan manoma ne ya sanya aka kawo taraktoci jihar domin tallafa musu.

A jawabin Lamidon Adamawa, Dokta Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa ya yi kira ga manoman su yi amfani da taraktocin ta hanyar da ta dace sannan ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa irin wannan babban tallafin da ta yi wa jihar.