Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatar Lafiya ta kashe sama da Naira biliyan hudu wajen kai dauki don warware matsalolin mutanen da ke bukatar agajin gaggawa a Arewa maso Gabas. Ministan Lafiya, Farfesa Isaac Adewole ya bayyana haka a ranar ayyukan jinkai ta duniya a Abuja. An yi amfani da kudin ne wajen sayen kayan tallafi da suka hada da magunguna da kayan aikin kula da lafiya da kuma horarwa da tura ma’aikatan lafiya masu aikin sa-kai. Ya nanata cewa matsalolin da ake fama da su sun hada da wadanda suka auku kwatsam da kuma na dogon lokaci da aka dade da su, don haka ma’aikatar ta bullo da ingantattu dabaru na tunkarar matsalar, ta hanyar samar da kayan aikin kiwon lafiya don duba mutanen da suka jikkata, sannan a bunkasa harkokin kula da lafiya a yankin.
Ministan ya ce Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta tunkari matsanancin halin ayyukan jinkai a Najeriya da kyakkyawar kula, ta hanyar inganta sashen aiwatar da ayyuka na musamman da nada cikakken darakta da zai kula matsalolin kula da lafiya a ayyukan jinkai. Shirin inganta kula da lafiyar al’ummar Arewa maso Gabas da tsarin kawo daukin gaggawa na NEHSHRSP da aka bullo da shi da manufar kyautata tsarin kula da lafiya a yankin. Gungun masu kawo daukin gaggawa an dora masa alhakin fito da shirin kula da lafiya na tsawon wata shida da ciyar da Jihar Barno don warware matsalar tabarbarewar kula da lafiya da samar da abinci mai gina jiki. Shirin an bullo da shi, an tabbatar da aiwatar da shi, don haka aka fadada shi zuwa wasu watanni shida bisa la’akari da nasarar da aka cimmawa wajen samar da managarcin tsarin kula da lafiya ga al’ummomi.
A cewar Farfesa Adewole, daga cikin nasarorin da ma’aikatar ta samu a Arewa maso Gabas akwai shawo kan ciwon zazzabin cizon sauro da ya addabi kimanin mutum dubu 15 a cikin garuruwan da sansanin ’yan gudun hnijira suke; samar da kayan aikin tsara iyali a al’ummomin da sannsanonin ’yan gudun hijira suke, inda aka karade akalla mata dubu hudu; samar da managarcin tsarin awo ga masu juna biyu; karbar haihuwar jarirai kimanin 1,100, ta hanyar kwararrun ungozoma a al’ummomin da sansanonin ’yan gudun hijira suke.