✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun Maulidi

An ba da hutun don murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 16 ga watan Satumban 2024, a matsayin ranar hutu domin bikin maulidi na tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S.A.W).

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dokta Magdelene Ajani.

Sanarwar ta ambato Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubumbi Tunji-Ojo yana taya al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar fiyeyyen halitta.

Ya gargaɗi dukkan ’yan Najeriya da su zama masu haƙuri da juriya tare da koyi da kyawawan dabi’u na Annabi, yana mai cewa yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Nijeriya.

Ministan ya buƙaci ’yan Najeriya da su ribaci wannan lokacin wajen yi wa ƙasar addu’ar zaman lafiya.