✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Soji a Sudan ta kori duk shugabannin jami’o’in kasar

An kori duk shugabannin jami’o’in kasar 30 tare da maye gurbinsu da wasu sabbi.

Gwamnatin Sudan wadda sojoji ke jagoranta ta kori duk shugabannin jami’o’in kasar 30 inda ta maye gurbinsu da wasu sabbi.

Jagoran Gwamnatin Sojojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan ne ya dauki wannan mataki bayan ya yi amfani da wata dokar soja inda ya ruguza Kwamitin Amintattu na Jami’o’in.

Tun watan Oktoban 2021 yake amfani da dokar soja bayan sun kawar da gwamnatin rikon-kwarya da Firaminista Abdallah Hamdok yake jagoranta.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa, Farfesoshi a Jami’ar Sudan University sun ce za su soma yajin aiki domin birjire wa wannan mataki.

Kamfanin ya ambato shugaban jami’ar Khartoum yana bayyana matakin Janar Burhan a matsayin wanda bai halasta ba.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa jami’o’i da makarantu na cikin ’yan gaba-gaba a zanga-zangar da ake yi domin kyamar mulkin sojin Sudan.