Gwamnatin Sudan wadda sojoji ke jagoranta ta kori duk shugabannin jami’o’in kasar 30 inda ta maye gurbinsu da wasu sabbi.
Jagoran Gwamnatin Sojojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan ne ya dauki wannan mataki bayan ya yi amfani da wata dokar soja inda ya ruguza Kwamitin Amintattu na Jami’o’in.
- Mutum 20 sun mutu a ruwa yayin tsere wa harin ’yan bindiga a Neja
- ’Yan sanda sun dakile wani hari kan matatar Dangote
Tun watan Oktoban 2021 yake amfani da dokar soja bayan sun kawar da gwamnatin rikon-kwarya da Firaminista Abdallah Hamdok yake jagoranta.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa, Farfesoshi a Jami’ar Sudan University sun ce za su soma yajin aiki domin birjire wa wannan mataki.
Kamfanin ya ambato shugaban jami’ar Khartoum yana bayyana matakin Janar Burhan a matsayin wanda bai halasta ba.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa jami’o’i da makarantu na cikin ’yan gaba-gaba a zanga-zangar da ake yi domin kyamar mulkin sojin Sudan.