Gwamnatin Sakkwato ta ce za ta kashe Naira biliyan 6.7 domin ciyar da marayu da talakawa a watan Azumi na Ramadan.
A cewar gwamnatin, ciyarwar ta haɗa da rabon hatsi da kuma dafaffen abinci, wanda za a raba a cibiyoyin rabon abinci da ke faɗin jihar.
- Ban mayar da hankali kan ɗora wa gwamnatin da ta shuɗe laifi ba —Tinubu
- Sojin Nijar za su saki Bazoum
Gwamna Ahmed Aliyu ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da rabon hatsin ga marayu da marasa ƙarfi 18,400 a faɗin jihar, inda ya ce kowannensu zai samu buhun shinkafa, da na gero da kuma N5,000.
A nasa bangaren Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya gode wa Gwamnan bisa ƙoƙarinsa na ɗabbaka wannan shirin, tare da tabbatar masa da goyon bayansa wajen inganta rayuwar al’umma.