Gwamnatin Jihar Kano ta tsare fitaccen mawakin yabon Manzon Allah (SAW), Malam Bashir Dandago.
A ranar Laraba Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano za ta gurfanar da Bashir Dandago a kotun da ke Nomansland a garin Kano.
- An kama mutumin da ke sayar wa da ’yan bindiga a Kano
- Yadda mutanen Jingir suka yi wa ’yan bindiga kofar rago
- Budurwa ta yi garkuwa da saurayinta don ta samu kudin biki
Hukumar ta kama mawakin ne bisa zargin sakin wata waka ba taer da izini ba, wadda a cikinta yake zagin malaman da ke kalubalantar Sheikh Abduljabbar Naisru Kabara.
Da take tabbatar da tsare Bashir Dandage, Hukumar ta ce wakar da makawkin ya fitar na iya tayar da rikici.
“Ya fitar da wata wata da a cikinta yake zagin mutane karara, wadda kuma ke iya tayar da rikici.
“Laifinsa shi ne fitar da wakar ba tare da samun sahalewar hukumar ba. Ba za mu bari mutane su rika zama kara zube ba.
“Za mu gurfanar da shi a kotu wadda ita ce za ta yanke hukunci daidai da laifinsa,” inji Shugaban Hukumar, Isma’il Na’abba Afakallah.
Idan ba a manta ba takaddama ta barke tsakanin malamai da Sheikh Abdujabbar wanda suke zargi da yin batanci ga Manzon Allah (SAW).
Tun a lokacin Gwamnatin Kano ta rufe masallaci da majalisan malamin wanda kuma ta haramta wa gudanar da duk wani nau’i na da’awa a fadin Jihar, har sai an kammala bincike.
A baya Gwamantin ta shirya gudanar da mukabala kan batun tsakanin malamn da Abduljabbar wanda ya ce ba a yi masa adalci ba a dakatarwar da aka yi masa.
Da farko kotu ta dakatar da gudanarda mukabalar kafin a halin yanzu ta ba da damar a gudanar.