✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kano ce silar ambaliya da rusau a Kofar Mata —IKMA

Kungiyar Cigaban Kofar Mata ta dora laifin ambaliyar ruwa da rushewar gidaje a unguwar kan Gwamnatin Jihar Kano

Kungiyar Dalibai a karkashin inuwar Kungiyar Cigaban Kofar Mata (IKMA), ta dora laifin ambaliyar ruwa da kuma rushewar gidaje a unguwar kan Gwamnatin Jihar Kano.

A wata sanawar da kungiyar ta fitar a ranar Laraba ta hannun kakakinta, Usman Bello Kofar Mata, ta koka bisa yadda aka gine duk wani fili da ke unguwar musamman wanda ke kallon filin wasa na Sani Abacha.

Babban takaici, a cewarta shi ne wani fili da ake zubar da shara da ’yan unguwar suka ce gwamnatin jihar ta sayar da shi ga wani.

“Wayar gari kawai muka ga an katange shi, yanzu babu inda za mu zubar da shara kuma babu mamaki shaguna za a gina wurin ” in ji shi.

Sannan ya ce, yanzu mutane a bakin titi suke zubar da shara da kuma magudanan ruwa, wanda bai kamata ba, amma babu yadda za su yi.

“Wannan da sauran wurararen da gwamnatin ta sayar a unguwar, yawancinsu a kan hanyoyin ruwa ne, ko kuma sun matse kwatocin da ruwa ke wucewa, hakan kuma ya haifar da ambaliyar ruwa, da kuma rushewar wasu gidaje,” a cewar kungiyar.

A karshe ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta duba lamarin, domin sun kai kokensu Maikatar Muhalli da ta Lafiya, har yanzu shiru.