✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da sace daliban firamare

Mahara sun kutsa makarantar firamare suka yi tisa keyar malamai da dalibai a Birnin Gwari

Gwamatin Jihar Kaduna ta tabbatar da rahoton da ke cewa maharan sun yi garkuwa da daliban firamare da malamansu a kauyen Rama da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar.

Aminiya ta kawo rahoton yadda sun yi ’yan bindiga suka yi garkuwa da malamai uku da dalibai a makarantar firamaren LEA da ke unguwar Rama mai nisan kilimita biyar daga garin Birnin Gwari a safiyar Litinin.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce sun samu rahoton garkuwa da daliban da malamansu, “Kuma rahotannin wucin gadi sun nuna abin ya faru ne a makarantar firamare ta LEA da ke kauyen Rema a Karamar Hukumar.”

Aruwan ya ce suna ci gaba da tattara bayanai game da sace daliban sannan ya yi alkawarin cewa Gwamnatin Jihar za ta fitar da cikakken bayani “ba da jimawa ba”.

Mai Unguwar Rama, Abdulsalam Adam ya shaida mana cewa, “Na samu labari cewa sun tafi da malamai uku da dalibai amma muna kokarin tabbatar da ainihin abin da ya faru tare da ’yan banga, sauran jama’a kuma sun bi sahun ’yan bindigar.

Wani mazaunain garin, ya ce: “Daya daga cikinmu ya ga dansa sun dauke shi a kan babur.

“Mutane da yawa sun yi ta maza sun bi sawun maharan; Yanzu muna marantar; mun sa a kira jami’an tsaro amma ba su riga sun karaso ba,” a ceawrsa.

Mazauna garin Rama sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar auka wa makarantar ne da misalin karfe 9 safiyar Litinin a yayin da dalibai ke isa makarantar.

Shi kuma wani mazaunin garin Birnin Gwari ya ce ’yan uwansa na daga cikin malaman da aka yi garkuwa da su.

Karo na uku ke nan cikin kwana huku da ’yan bindiga ke kai wa makarantu hari a Jihar Kaduna.