✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Jigawa ta dukufa wajen gyaran makarantun ’ya’yan fulani – Shehu Garba Sakwaya

Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki matakin gaggawa wajen gyaran makarantun ’yayan fulani makiyaya 80 da suke cikin wani hali na rashin gyara daga cikin makarantun…

Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki matakin gaggawa wajen gyaran makarantun ’yayan fulani makiyaya 80 da suke cikin wani hali na rashin gyara daga cikin makarantun ’ya’yan makiyaya 350 da jihar ke da su.

Shugaban Hukumar Kula da Makarantun ’Ya’yan Makiyaya na Jihar Jigawa Malam Shehu Garba ne ya sanar da haka a wata hira da ya yi da wakilinmu a Jihar Jigawa.

Ya kuma kara da cewa kalilan ne cikin makarantun suke a lalace ba duka, kuma suma tuni gwamnatin jihar ta ware wasu makudan kudade da za a gyara su.

Ya kara da cewa saboda a kara wa yaran fulanin sha’awar karatu ne ya sa gwamnatin jihar ta dinka wa musu kayan makarantar, ta ba su jakankunan zuwa makarantar da littatafan karatu da rubutun kyauta.

Ya kuma ce ita ma Gwamnatin Tarayya ta gina ajujuwa uku a makarantar ’ya’yan makiyaya da ke Bamaina tare da gina bandaki a makarantar a karkashin Hukumar Bada Ilimin ’Ya’yan Makiyaya ta kasa.

Sannan sai ya bukaci gwamnatin jihar ta samar da karin malamai kwararru a makarantun.