Gwamnatin Jihar Gombe karkashin Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo ta yi alkawarin samarwa Malaman Makarantu a jihar wani tsarin alawus-alawus na musamman don Malaman da aka tura makarantun dake yankunan karkara don karfafa musu gwiwa.
Wannan batun ya fito ne ta bakin Kwamishinar Ilimi ta jihar, Hajiya Aishatu MB Ahmed, a lokacin da take zantawa da wakilinmu a Gombe bayan an gudanar da bikin ranar malamai ta duniya mai taken ‘Samarwa Malamai Yanci’.
Hajiya Aishatu MB Ahmed, ta ce wannan alawus din an shirya za a fara bai wa malaman da suka yarda suke zuwa kauyukan da ake tura su ne domin wasu da yawa ba sa yarda su je kauyukan da ake tura su don koyarwa.
Ta ce da zarar an fara bayar da irin wannan alawus din ga malamai hakan zai sa duk wani malami da aka yi wa canjin wajen aiki zuwa karkara ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ya amince da canjin da
aka masa.
Kwamishinar ta kara da cewa gwamnati ta samar da makarantu irin na zamani a ko’ina a fadin jihar har da kananan hukumomi ga kuma kayayyakin aiki, amma saboda wani dalili marar tushe sai ka ga malamai sun ki amincewa.
A gefe guda da take Karin haske kan Malaman dake korafi game da rashin sanin makomar su wadanda aka rike mu su albashi da sunan ma’aikatan bogi, ta ce kwamiti ne aka kafa wanda ya yi aikinsa ba tare da son rai ba, ya bi ko’ina dan tabbatar da an tantance malaman gaskiya da na boge.
“A lokacin da kwamitin ya bi dukkan kananan hukomomin jihar ya tarar da wasu wadanda matan Manyan mutane ne wasu ‘ya’yan ‘yan siyasa da aka dauke su aiki ba sa zuwa kuma duk an dakatar da su sannan an samu wata ma wacce mijinta ya tafi karatu a kasar Cyprus ta bishi bayan ba karatu take ba, kuma albashin ta na shiga ita ma kwamiti ya dakatar da ita,” inji Kwamishinar.
Daga nan sai ta ce ba an kafa kwamitin tantance ma’aikatan ba ne dan cin zarafin wani ko wasu ba, an yi ne tsakani da Allah kuma wadanda abin ya shafa kuma ba su da laifi tuni aka fara biyansu albashinsu na watanni bakwai zuwa takwas da ba a biya su ba.