✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Buhari ta gaza a fuskar tsaro- Kadaria Ahmed

Fitacciyar ‘yar jaridar nan mai suna Kadaria Ahmed, ta bayyana cewa shugaban Najeriya Buhari, ya gaza a fannin tsaron kasa, ta ce harkar tsaro abu…

Fitacciyar ‘yar jaridar nan mai suna Kadaria Ahmed, ta bayyana cewa shugaban Najeriya Buhari, ya gaza a fannin tsaron kasa, ta ce harkar tsaro abu ne na gwamnatin tarayya da bai kamata ayi sako-sako da shi ba.

“A gaskiya Baba Buhari ya gaza a harkar tsaro, abin mamaki a baya ma cewa ya yi, bai ma san matsalar Boko Haram bata gyaru ba, kaga a she ba a fada masa gaskiyar lamarin kenan, kuma bai san me kasa ke ciki ba, to ya za a yi kana shugabancin kasa amma baka san me take ciki ba?” In ji ta.

Kadariya Ahmad, ta bayyana hakan ne a safiyar ranar Laraba a zantawarta da manema labarai a ofishin ta a Legas, ta ce Shugaba Buhari bai yi kokari a harkar tsaro ba, ko da yake a baya an sami sauki a jihohin Barno da sauran wuraren da ke fuskantar rikicin Boko Haram.

Amma a yanzu hannun agogo na komawa baya, “Kaga yanzu bai wuce kwana uku ba da aka kashe sama da mutum 30 a Borno, dan haka na fada na kuma sake fada ya kamata shugaba Buhari, ya canza manyan jami’an da ke kula da sha’anin tsaro domin da alama wannan aikin yafi karfin su, idan ba zasu iya ba, su matsa su bai wa wasu sababbi dama, domin su tuni lokacinsu ya cika.”