✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta yi watsi da masu kiwon kaji – Abdulrahman Lawal

Wani fitatcen mai kiwon kaji a jihohin Bauchi da Filato kuma mai gonar kiwon kajin nan ta Yankari Farms da ke karamar Hukumar Toro a…

Wani fitatcen mai kiwon kaji a jihohin Bauchi da Filato kuma mai gonar kiwon kajin nan ta Yankari Farms da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Alhaji Abdulrahman Lawal ya ce duk da kokarin da wannan gwamnati take yi, wajen bunkasa harkokin noma a kasar nan, ta hanyar tallafa wa manoman kayayyakin yin gona a bangarori daban-daban, amma ta yi watsi da masu kiwon kaji.                  Alhaji Abdulrahman Lawal ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya, inda ya ce “Wallahi mu masu kiwon kaji gwamnati ba ta shirya mana komai don tallafi  ba a cikin wannan tafiya da ake yi, na tallafa wa manoman kasar nan.”

Alhaji Abdulrahman ya ce ana ta kiran kowa a bangarorin manoma  ana ba su tallafin  injinan ban-ruwa da taki da magungunan feshi da kudi. Amma ba a kula da masu kiwon kaji ba.

Har’ila yau ya ce “Ka dubi lokacin da muka yi asara a annobar murar tsuntsaye da aka yi a kasar nan, sai da muka yi shekara uku, ba a ba mu tallafin ko kwabo ba.”

Ya ce masu gidajen kaji da dama sun rufe gonakinsu, saboda mawuyacin halin da suka shiga a kasar nan, sakamakon rashin tallafin da ake yi musu. Don haka yanzu kiwon kaji ya yi baya a kasar nan.

Ya ce taimakawar da harkokin kiwon kaji yake yi wajen bunkasa harkokin noma a kasar nan yana da yawa. “Yau masarar da ake nomawa a Najeriya idan ba don masu kiwon kaji ba, sai dai aje a zubar da ita, domin  kashi 95 na masu zuwa kasuwannin kasar nan, suna sayen masara, masu kiwon kaji ne. Don haka masu gidajen kaji ne suke cin masara da waken soya da kulikulin da ake yi a kasar nan. Baya ga kashin kajin da muke fitarwa wanda manoma suke amfani da shi wajen gudanar da harkokin nomansu,” inji shi 

Alhaji Abdulrahman ya ce idan aka ce babu kwai a Najeriya, wane irin hali ne za a shiga? Sannan ga wadanda suke sayen kwan nan suna tafiya da shi lungu-lungu na kasar nan. Baya ga ma’aikatan da masu gidajen kajin suke dauka aiki.

Ya ce tallafi na farko da za a yi wa masu kiwon kaji a kasar nan shi ne a yi musu inshora ta gaskiya, wanda za a rika biyansu, idan wata asara ta taso musu. Baya ga haka gwamnati ta rika sayen masara a wajen manoma tana sayar musu kan farashi mai rahusa, domin su ji dadin gudanar da wannan sana’a  cikin sauki.