Gwamnatin Tarayya ta rufe sayar da sabbin layukan waya da kuma yin rajistan layukan waya nan take a fadin Najeriya.
Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ce ta ba da umarnin ga kamfanonin sadarwa har sai ta gama tantance layukan wayan da ake amfani da su a kasar.
Ta ce Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Ali Pantami ne ya sa a tantance layukan wayan da ba a yi wa cikakken rajista yadda ya kamata ba.
Sanarwa da Daraktan yada labaran NCC, Ikechukwu Adinde, ya fitar ta ce yin hakan ya zama dole kuma duk kamfanin da ya saba, to zai yaba wa aya zaki, da zai ga soke rajistarsa.
Sai dai ya ce akwai yiwuwar yin rangwame ga wasu, amma da izinin Gwamnatin Tarayya ta hannun hukumar ta NCC.