Ministan Sadarwa na Najeriya, Isa Ali Pantami ya ce Gwamnatin Tarayya ta dakatar shirin karin kudin da harajin kiran waya da na data da kamfanonin sadarwa suka so a kara.
Pantami ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a wani taron kaddamar da Kwamitin Shugaban Kasa na sa harjai kan hayoyin sadarwa na zamani a Abuja a ranar Litinin.
- ‘Najeriya na fuskantar barazanar tsaro mafi girma tun bayan Yakin Basasa’
- Mutum 8 sun nitse a ruwa a Jigawa
A baya dai Minista Pantami ya soki shirin kara wa harkar sadarwar haraji wanda ya ce wani karin nauyi ne a kan wannan bangare na tattalin arziki.
Ministan a bisa ra’ayin kansa bai goyi bayan matakin sa harajin ba, wanda zai sa kudin kiran waya da na data su karu.
Sannan ya kuma ce, ya ba Shugaba Buhari shawarar yin watsi da batun yin karin, la’akari da irin tasirin da hakan zai yi a kan tattalin arziki da fasahar sadarwa.
Pantami ya kuma ce, ce ba a tuntubi Majalisar Dokoki ba kan batun.
Sai dai Ministar Kudi da Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ta zargi Pantami da kokarin yin zagon kasa ga Gwamnatin Tarayya a kan lamarin a baya.