✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati na son a rage amfani da injinan janareta barkatai a Najeriya

Gwamnatin ta ce har yanzu haramcin shigo da injinan na nan daram.

Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi akan yawan amfani da injinan janareta masu hayaki barkatai musamman a birane saboda illar da suke da ita ga muhalli.

Shugaban Hukumar Kula da Ingancin Muhalli ta Kasa (NESREA), Farfesa Aliyu Jauro ne ya yi gargadin yayin tattaunawarsa da Aminiya a Abuja.

A cewarsa, yawan amfani da injinan wanda a yanzu ya tasamma zama na gasa na taka muhimmiyar rawa wajen gurbata yanayi da kuma muhalli, inda ya yi kira da a kaurace wa amfani da su.

Ya ce, “Duk da dai na san mutane na amfani da su ne saboda rashin cikakkiyar wutar lantarki, amma zasu iya komawa amfani da na’ura mai amfani da hasken rana.”

Ya kuma tunatar da ’yan Najeriya cewa har yanzu haramcin da gwamnati ta sanya a kan shigo da injinan na nan daram, kuma nan ba da jimawa ba hukumar zata fara dirar mikiya a kan masu kunnen uwar shegu.

Shugaban hukumar ya kara da cewa, “Muna da wani shiri da zamu bullo da shi nan ba da jimawa ba da zai magance amfani da injinan janareta, ko da yake muna tunanin farawa da manyan injinan, kafin mu koma kan kanana.

“Muna kuma duba yuwuwar hada duka biyun. Zamu tabbatar mutane sun rage yawan amfani da janareta mai hayaki saboda illarsa ga muhalli.