✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Sakkwato ya nada Sakataren Gwamnati da karin wasu mukamai 7

Gwamnan ya nada Muhammad Bello Sifawa a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar

Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya nada Muhammad Bello Sifawa a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar.

Kazalika, Gwamnan ya nada karin wasu mukamai guda bakwai masu muhimmanci, kamar yadda mai magana da yawunsa, Abubakar Bawa ya tabbatara a cikin wata sanarwa ranar Laraba.

Sanarwar ta ce Gwamna Ahmed ya kuma nada Aminu Dikko a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.

Sauran mukaman da aka nada sun hada da babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin gudanarwa, Barista Gandi Umar Muhammad, sai Alhaji Hussaini Gorau babban mataimaki na musamman ga Gwamna.

Gwamnan ya kuma nada Bello Yahaya Wurno a matsayin babban mataimaki na musamman kan huldar gwamnati, yayin da ya nada Faruk Labbo da Faruk Ahmad Shuni dukkansu an nada su mataimaka na musamman su ma.