✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Jihar Rivas ya gana da Cristiano Ronaldo

A ci gaba da shirye-shiryen habbaka wasanni a Jihar Rivas, gwamnan jihar Nyesom Ezenwo Wike ya gana da Cristiano Ronalda da sauran ‘yan wasan kungiyar…

A ci gaba da shirye-shiryen habbaka wasanni a Jihar Rivas, gwamnan jihar Nyesom Ezenwo Wike ya gana da Cristiano Ronalda da sauran ‘yan wasan kungiyar Real Madrid a kasar Spain.

Gwamnan ya yi takanas-ta-Kano ne zuwa kasar Spain domin neman hadin gwiwa da kungiyar ta Real Madrid domin hakkaka wasannin jihar kamar yadda mataimakin gwamnan na musamman a kan harkokin yada labarai ta kafofin zamani Simeon Nwakaudu ya sanar.

A cewar gwamnan, “Muna amfani da wasan kwallon kafa ne a matsayin daya daga cikin harkokin qarfafa wa matasa gwiwa. Burin mu shi ne mu samar da ‘yan wasan kwallon kafa da duniya za ta yi alfahari da su nan gaba,” inji Wike.

Daga cikin wadanda suka raka gwamnan zuwa kasar ta Spain akwai, kwamishinan wasannin jihar Mista Boma Iyaye, da tsohon dan wasan Najeriya Adokiye Amiesimaka.