✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Jihar Jigawa zai gina wa kananan ’yan kasuwa shaguna

Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya ce zai gina wa kananan ’yan kasuwa rumfuna irin na zamani domin bunkasa  harkokin kasuwanci a jihar.Shugaban Hukumar…

Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya ce zai gina wa kananan ’yan kasuwa rumfuna irin na zamani domin bunkasa  harkokin kasuwanci a jihar.
Shugaban Hukumar Raya birnin Dutse (DCDA) Malam Abdullahi Bello ya shaida wa wakilinmu haka a wata ganawa da ya yi da shi a ofishin hukumar a ranar Litinin da ta gabata.
Ya kara da cewa wadanda za su amfana da shagunan mafiya yawansu mazauna wurin, ko a wurin suke yin sana’a. Ya ce  sauran wadanda za su ci moriyar shagunan sun hada da wanzamai da masu wankin takalmi da masu shayi da rake har ma da Fulani masu tallan nono.
Har ila yau, ya ce za a raba shagunan kyauta ne gama su bukata, amma dole masu sha’awar shagunan su rubuta a rubuce su mika takardun ga ofishin hukumar.
Daga nan ya bayyana cewa ko wanne shago za a gina shi ne a kan Naira dubu 70. Kuma ana sa ran za a kashe fiye da miliyan uku wajan gina shagunan.
A karshe ya ce ana fatan kammala aikin ginin shagunan nan da watanni biyu masu zuwa. Kuma dazarar an kammala za a raba wa wadanda suka gabatar da takardun bukatar neman shagunan.