Mai karatu Alhamdulillah da Allah SWT ya nuna mana wannan makon kuma kamar yadda na yi alkawari as yau zan dora akan inda na tsaya. Idan mai karatu bai manta ba. Na tabo batutuwan da suka shafi kasa daure adawa ga Gwamna Ibrahim Shehu Shema walau daga `yan jam`iyyarsa ta PDP, ko na abokan hamayya ko ta abokan aikinmu manema labarai. Mai karatu bisimillah.
A farkon wannan shekarar da rana tsaka Gwamna Shema, ya hana motocin sufurin da Alhaji Muntaka Darma tsohon Babban Sakatare na Hukumar Asusun kula da Kimiyar harkokin man fetur wato PTDF, da ya sayo da kudinsa, ya sanya su haya don taimaka wa zirga-zirgar al`umma cikin rahusa a birnin Katsina da kewaye. Motocin da ala tilas bisa ga karfin gwamnati suka daina zirga-zirga a titunan babban birnin jihar. Babban zargin da Gwamnatin Shema ta yi wa Alhaji Muntaka Darma shinena wai ya zo ne don ya nemi mikamin gwamnan jihar a inuwar jam`iyyarsu ta PDP.
Yanzu mu dawo akan TATA, wanda duk dambarwar da ake da shi ban taba yarda da cewa da sa hannun Gwamnatin Shema ba, sai a yayar wannan jaridar ta Weekly Trust, ta ranar 08-11-14, a shafi na 7, inda na karanta martanin Shugaban Ma`aikatan Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Yusuf Salisu Majigiri da wani Alhaji Halliru Magaji, wadanda suke bayyana yunkurin neman takarar TATAN da tamfar wanda ya rude, ta yadda wai har ya kasa halartar taron zaben Wakilan da za su zabi dan takarar neman mukamin gwamnan a cikin jam`iyyar ta PDP da aka yi a dukkan fadin jihar ta Katsina a ranar Asabat din wancan makon, amma wai ya tafi yana yakin neman zabe. Abin tambaya a nan shi ne, ta ya ya su Honorabul Majigiri suke tsammanin TATA ya je wajen taron zaben wakilai, alhali kamar yadda rahotanni suka gabata, rahotannin da ya zuwa yanzu Gwamnatin Katsina da jami`anta ba su musanta zarge-zargen da TATAN ya yi musu kan sun hana a daura aurensa a cikin babban birnin jihar da fadin Jihar Katsina kaf, dole sai Kaduna aka tafi? Haka kuma TATAN, ya zargi gwamnatin da mukarrabanta da ba ma hana shi suka yi ya kaddamar da taron gangamin aniyar neman takararsa ba, a`a, hatta shirin wurin taron da ya yi a filin Folo an bata kayayyakin, wasu ma ya ce kona su aka yi, baya ga hana jirgin da ya kawo shi da magoya bayansa sauka a filin jirgin saman Katsina a ranar.
A gefe daya kuma wasu da suke kiran kansu masu ruwa da tsaki na jam`iyyar PDP dana al`ummar gari, irinsu Sanata Umaru Tsuri, sun ci gaba da yin kamfen akan TATAN ba shi da wani abu da zai tabukawa Jihar Katsina muddin ya ci gwamnan jihar sai ma ya yi sama da fadi da kudinta, bisa ga la`akari da irin dimbin kudaden da yake batarwa yanzu a cikin yakin nemn zabensa. Abinda na yi tsammanin shi ne su Sanata Tsauri su mayar da hankali wajen adawa da takarar TATA, shi ne, su nuna rashin cancantarsa kasancewar ya fito daga shiyyar da take ta mulkin jihar Katsina (duk da tsarin mulki bai mai takunkumi akan haka ba), shiyyar da tunda aka sari Jihar Katsina a kuma cikin mulkin dimokuradiyya ita take gwamnan jihar (Alhaji Sa`idu Barda 1992 zuwa 1993; Alaji Umaru Musa `Yar`aduwa 1999 zuwa 2007; Barista Ibrahim Shehu Shema 2007 zuwa yau). Amma ba su buge da ina TATA ya samo kudinsa ba, ko don shi ba shi da lasisi irin wanda shugaban kasa da gwamnonin jihohi suke da shi na su dulmiya hannayensu cikin lalitar gwamnatocin da suke mulki, su batar akan yadda ransu ya raya masu?
Abin da ni da masu ra`ayi irin nawa mu ka so mu ji daga Gwamnatin Jihar Katsina da mukarrabanta da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki na jihar dana cikin jam`iyyar PDP, shi ne ga laifin da TATA ya yi, amma ba wai yana kashe kudade ba, ta hanyar aurar da zawarawa da gina assibitocin sh- ka-tafi da masallatai da bayar da tallafin ababen hawa da sauran taimako, kamar yadda aka san mai neman takarar wani mukami, ko mai rike da mukamin siyasar ya saba yi a wannan jamhuriyar. Kuma a lokaci irn wannan na kakar zabubbukan kasa. Amma batun yana son ya kaddamar da takararsa alhali lokaci bai yi ba, ko kuma tuhumar ina ya samo kudinsa, duk ba batutuwa ba ne a wannan lokaci. Me ya sa irin nwadannan mutane suka je kaddamar da neman takarar shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan? Ko kusa ba ina daure wa mutane irinsu TATA gindi ba ne su yi ta barin kudi, amma ina son mu kalli wannan al`amari da idon basira.
Mene ne ma abin rigima a wannan jamhuriyar, alhali ga tarihinan barkatai na irin kiyayyar da wasu gwamnoni ko `yan jam`iyya suka nuna wa wasu daga cikin wadanda suka nemi su gaje su. Ya ya gwamna Adamu Ma`azu na jihar Bauchi ya karke da gwmnan jihar mai ci yanzu Malam Isa Yuguda, wanda bayan Minista, har karo biyu a cikin Gwamnatin Obasanjo a zaman wakilin Jihar Bauchi, amma da ya fito ya ce yana son gwamnan jihar ai Gwamna Ma`azu a lokacin cewa ya yi Malam Isan ba ma dan asalin Jihar Bauchi ba ne, amma da Allah Ya ce sai Malam Isan ya zama gwamna ai ya zama. Mu je Jihar Sakkwato, ya Gwamna Alhaji Attahiru dalhatu Baffarawa ya karke da mataimakinsa a lokacin, Gwamna Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako a jam`iyyarsu ta ANPP, ai har shiryawa ya yi da `yan Majalisun Dokokin jihar don su tsige Wammakon, amma Wammakon ya sauka daga kan mukaminsa, ya kuma samu takara a jam`iyyar PDP a 2007, a dole Gwamna Bafarawa ya mika ragamar mulkin ga Wammakon.
Isharori na nan fululu a cikin wannan jamhuriya ga masu hadamar mulki, da ya kamata su zame mana ishara, amma shaidanu na mutane da aljannnu, ba sa barin masu mulki su dube su da idon rahama bare su yi aiki da su. Shi kansa Gwamna Shema ya san yadda aka kakaba wa mutanen jihar shi, ta yadda har kirari ake yi masa a lokacin na “Shema Gwamnan dole ana sa fastarka ana kuka,” amma da Allah Ya ce zai yi, wa ya hana.
Ina taya gwamna Shema murna da Allah Ya buda masa kirjinsa ya fara bullo da tsarin mulki a shiyya-shiyya da a wannan karon ya dauko na shiyyar mazabar dan Majalisar Dattawa ta Daura, inda ya dauko Injiniya Musa Nashuni Kwamishinansa na Inganta ma`adanai da ya fito daga waccan mazaba. Ba wai inamurna ne ba don Injiniya Nashuni ya fito daga Kantin Kankiya inda aka haife ni ba, a`a ina murna ne da Allah Ya nuna mana irin wanna lokaci. Su ma mutanen mazabar dan Majalisar Dattawa ta Katsina ta kudu (Karaduwa), da yardar Allah a gaba sai a yi da su. Ga Gwamna Shema ina dai kira da kada ya bata rawarsa da tsalle. Lokaci ya yi da zai rage zazzafar adawarsa, ko don burin da yake da shi na ya mallaki kasar nan. Don haka lallai ya san yadda zai zauna da mutanensa lami lafiya.