✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Bagudu na shirin magance matsalolin shekaru aru-aru – Sardaunan Kende

Jihar Kebbi na daya daga cikin jihohin Najeriya da aka samu canji a akalar shugabanci daga gwamnatin PDP zuwa gwamnatin APC, sai dai duk da…

Jihar Kebbi na daya daga cikin jihohin Najeriya da aka samu canji a akalar shugabanci daga gwamnatin PDP zuwa gwamnatin APC, sai dai duk da haka, har yanzu wasu mutane na ganin babu bambanci daga tsohuwar gwamnatin da ta shude da ta kan karagar mulki a yanzu.

Amma ra’ayin ya saba ga wasu wadanda suke ganin yanzu Jihar Kebbi ta samu hazikin shugaban da yake sauraren shawara, tare da aikata abin da aka bashi shawara don ciyar da jiharsa gaba. Ga bayanin da Alhaji Abu Hali Sardaunan Kende, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na yankin Kebbi ta Arewa ya yi a hirarsa da wakilinmu.
Aminiya: Ya kake ganin kamun ludayin wannan gwamnati fiye da watanni hudu na shugabancin Gwamna Atiku Bagudu a Jihar kebbi.?
Sardaunan Kende: Bissimillahir Rahamanir Rahim. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mai iko da iyawa, wanda mulki da iko da rahamarsa ne suka game duniya baki daya. Salati da sallama ga ma’aikin Allah, Annabin Rahama Muhammadu (SAW), wanda daraja da kwarjininsa ya hade kowa da komai a wannan duniyar tamu da gobe kiyama.
Na ji dadi da ka yi mani wannan tambaya, ganin cewar, Gwamnatin Mai girma, Atiku Bagudu ba ta dade da fara aiki ba, kuma tana da shekaru hudu a nan gaba, don samar da ayyukan raya kasa da ci gaban al’ umma a wannan jihar tamu mai albarka.
Watanni hudu daga cikin shekaru hudu ba su wuce cikin cokali wajen gano ko hukunci a kan lamarin mulki da ayyukan raya kasa na kowace gwamnati ba. Amma kuma duk da wannan, hakika jama’ar Jihar kebbi sun san yanzu sun samu gwamnati mai sauraren matsalolinsu da kuma jin kokensu don magance matsalolin da ke addabarsu shekaru aru-aru.
Aminiya: Wasu na ganin Gwamna Atiku bai aiwatar da wani abin a zo a gani ba cikin watanni hudu da ya yi yana mulki?
Sardaunan Kende: Ba haka abin yake ba, idan ka fahimci bayani na a baya, ina nufin har yanzu idan mutane suka fahimta akwai ayyukan da yake ana aiwatarwa, amma ba kai tsaye za a iya ganin amfaninsu ba, don su kan dauki lokaci wadansu daga cikin ayyukan da Gwamna Atiku Bagudu ya aiwatar sun kunshi magance matsalar rashin tsabta da ta addabi babban Birnin jiha, da kuma farfado da gyara tsarin ilimi, da gyara wutar lantarki awa 24 ba a dauke wuta da sawo tirsifomomi guda 150, domin kara inganta wutar lantarki, ya kuma biya ma’aikatan jihar da na kananan hukumomi tun daga matakin farko har zuwa karshe kudin hutunsu, ana kuma biyan albashi akan kari tun daga 25 ga wata.
Ba nan Gwamna Atiku kawai ya tsaya ba, ko da ya zo ya cimma bashi na ba ’yan makarantar sakandare abinci sama da Naira biliyan biyu da kuma bashin kudin ’yan makaranta na gaba da sakandare da jami’o’i, amma yanzu duk ya ba da izinin a biya ba tare da vata wani lokaci ba, da kuma biyan kudin fensho da bai wa ma’aikatu kudin tafiyar da harkokin yau da kullum, savanin waccen gwamnati da ta gabata. Akwai sake tayar da komadar tattalin arziki wajen hada kai da ’yan kasuwa don ciyar da Jihar Kebbi gaba.
Haka ma tun hawansa bisa karagar mulki, Gwamna Atiku Bagudu ya bayar da fifiko ga nemo hanyoyin shawara don inganta tarbiyyar matasa da kuma kyautata wa al’umma, tare da hana satar dukiyar kananan hukumomin mulki da biyan hakkokin ma’aikata akan ka’ida.
Haka kuma ya bayar da Naira miliyan-goma-goma ga kowace karamar hukuma ,domin raba wa al’umma a lokacin babbar sallar da ta gabata.
Aminiya: Wasu na cewa kullum Gwamna Atiku yana kukan ya gaji matsaloli,, ya kake ganin wannan al,amari?
Sardaunan Kende: Dole ne duk wata gwamnati da ta zo za a iya bayyana hakan, cewar akwai wata matsala da take addabar al’umma da ta gada daga gwamnatin da ta shude. Wannan ya shafi tattalin arziki da walwala da kuma tsaro. A Jihar Kebbi, babbar matsalarmu ita ce ta lalacewar sha’anin kasuwanci da tarbiyyar matasa da kuma rashin aikin yi da watsi da harkokin noma, wadannan su ne muhimman batutuwa da muke ganin yanzu a nan bai wa muhimmanci cikin dan kankanen lokaci, ana kokarin shawo kansu da kuma magance su, ta hanyar sanya wadanda suke da ruwa da tsaki a ciki domin komai ya tafi daidai.
Aminiya: Ya kake kallon gwamnatin ta fuskar tallafa wa jama’a da samar da ababen more rayuwa?
Sardaunan Kende: Idan za ka yi wa Gwamna Atiku Bagudu adalci, dole ne ka ba shi damar ya fahinci abin da ya tarar da kuma tsara hanyoyin da suka dace don tsamo wannan jihar daga tsohuwar hanyar da “yan siyasa suka sanya ta, ala dole komai sai an yi da su, kuma dole komai sai yadda suke so a yi.
Hulda tada Gwamna ta gaskiya ce, don kuwa tabbas abin da na zaba, na tabbata zaiyi mana adalci don kuwa ya nuna duk da sanyin halinsa, ya nuna mutum ne wanda ya san abin da yake yi da kuma aikata ayyukan cigaba a wannan jiha ta kebbi.
Na tabbata Gwamna Atiku Bagudu kamar yadda kowa ya sani dattijo ne a ayyukansa da kalamansa, mutum ne mai son bin ka’ida da kuma aikata gaskiya da adalci a lamuran yau da kullum. Wannan yana daga cikin dalilan da ya sanya ya yi fice tun lokacin shigarsa siyasa. Don haka yana da kalubale mai yawa da ke bukatar a yi masa addu’a da fatan alheri, don samun nasara da kuma ciyar da wannan jihar tamu agaba.
Aminiya: Duk wannan batu da kake yi, amma a gefe wasu na fadin sun gaji da gafara sa, ba su ga kaho ba?
Sardaunan Kende: tabbas akwai masu wannan ikirarin, amma bari in yi tsokaci ga wadanda suke cewa ba su san inda ya nufa ba. Ya kamata mutane su kalli gwamnatin yanzu da wadda ta gabata. Gwamnatin da ta gabata ta ce ta bar bilyoyin kudi a cikin lalitar gwamnati, kuma ba a binta wani bashi mai yawa, sai ga shi a binciken da Gwamna Atiku Bagudu ya yi ya gano cewa Jihar Kebbi dankare take da bashi na ’yan fensho da ma’aikata da kudin ’yan makaranta, tun daga sakandare har zuwa jami’o’i, sannan tsohuwar gwamnati ta yi awon gaba da kudin kananan hukumomi na gina filin jirgi da na tallafin man fetur (sure .p).
Aminiya: Me za ka ce a karshe?
Sardaunan Kende: Babu wani abu da ya rage illa al’ummar Jihar Kebbi su bai wa gwamna cikakken goyon baya domin ya kai ga gaci.
Sannan shi ma ya kula da mutanen da suka yi tsayuwar daka wajen tabbatar da cewar ya samu nasara, kada abin ya zama kura da shan bugu gardi da karvar kudi.
Kodayake nasan wannan gwamnati ba ta macuta ba ce, irin wadda ta shude a baya.