✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Ambode ya kara Inshorar ’yan sandan da suka mutu a bakin aiki

Gwamnan Jihar Legas, Mista Akinwunmi Ambode ya sanar da karin kudin inshorar ‘’yan sandabn da suka mutu a bakin aiki a Jihar Legas, inda ya…

Gwamnan Jihar Legas, Mista Akinwunmi Ambode ya sanar da karin kudin inshorar ‘’yan sandabn da suka mutu a bakin aiki a Jihar Legas, inda ya ce za a rika biyan iyalansu Naira miliyan 10.

Tsarin inshorar mutuwa ga ’yan sandan ba su da babbban matsayi bai wuce Naira miliyan guda ba, yayin da manyan jami’ai za a biya magadansu Naira miliyan biyu. Kuma ya ce kudin inshorar manya da kananan jami’an ’yan sandan duk ya zama bai daya, wato Naira miliyan 10
Gwamna Ambode ya bayyana karin kudin inshorar ne, a lokacin da yake karbar lambobin karramawa biyu a gidan gwamnati dake Ikeja. Ya kuma samu lambobin yabon ne daga daga Rundunar jami’an tsaron kawo daukin gaggawa ta Afirka ta Kudu (RRS), daga bangaren jami’an ’yan sandan su.
Ya nuna muhimmancin karin kudin inshorar ’yan sandan da suka mutu a bakin aiki ne, inda ya nuna alhininsa game da rasa rayukansu a bakin aiki. Don haka ya yi t akai kawo a bayanansa, saboda ya nuna muhimmancin biyan iyalan mamatan gwaggwaban kaso.