✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gudun ni’ima

Wani mutun ne ya ga hadari ya hadu, gari ya yi baki kirin sai ya kama hanyar gida yana ta sauri. Sai suka hadu da…

Wani mutun ne ya ga hadari ya hadu, gari ya yi baki kirin sai ya kama hanyar gida yana ta sauri. Sai suka hadu da wani mutum, ya ce: “Malam, ni’imar Allah za ta sauka kake gudunta?” Sai mutumin nan ya daina sauri, ruwan ya sauka ya yi masa dukan tsiya. Rannan yana zaune sai ya ga wannan mutumin da ya hana shi sauri yana ta sauri saboda ya ga hadari. Ya ce: “Malam rahama za ta sauka kana gudunta?” Sai ya ce: “Ina gudu don kada in taka rahamar ne.”
Daga danladi China, Kano 08034463170