Kungiyar Ci gaban Gombe ta Arewa (GONUDA) ta ce yankin na kan gaba wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Shugaban Kwanitin Amintattu na kungiyar wanda shi ne Walin Kwami Alhaji Muhammad Musa Kafarati ya bayyana haka a taron manema labarai da suka kira a Gombe.
Kungiyar GONUDA, ta kunshi kanana hukumomi biyar da suka hada da Gombe da Kwami da Dukku da Funakaye da Nafada kuma suna da yawan al’umma fiye da miliyan daya.
Ya ce a yankin ana noman rani da na damina sosai ga kuma albarkatun kasa masu yawa har da man fetur.
Kungiyar ta roki Gwamnatin Jihar Gombe cewa tunda yankin na fama da matsalar koma baya a bangaren ilimi sun nemi a sake bude makarantun sakandare na yankin da aka rufe shekarun baya lokacin rikicin Boko Haram kamar makarantar kwana ta GSS Dukku da Nafada da ta Malala.
Sun kuma koka kan lalacewar harkar kiwon lafiya a kananan hukumomi hudu.
Duk yawan al’ummar yankin kamfani daya take da shi na siminti na Ashaka, shi din ma Turawa sun mamaye shi babu ’ya’yansu da ke cin moriyarsa.
Kungiyar GONUDA ta kara da cewa yankinn Gombe ta Arewa na fama da matsalar rashin aikin yi a bangaren matasa kuma hakan na da nasaba ne da yadda mutane ke barin garuruwan suna dawowa fadar jihar.
Kungiyar ta ce matasan suna fama da matsalar shaye-shaye wanda ba komai ya haifar da hakan ba illa rashin aikin yi, amma GONUDA za ta hada kai da masu ruwa-da-tsaki wajen shawo kan matsalar da ya mayar da yankin baya.
Sannan sun shiga yarjejeniya da ’yan takara na wannan yankin kama daga Gwamna da Sanata da duk wani dan takara cewa idan suka ci zabe za su yi wakilci nagari da za su ciro yankin daga kangin da yake ciki.