✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Golden Balley Kafanchan ta lashe Kofin Zaman Lafiya na Lali

A ranar Juma’ar da ta gabata ce filin wasan kwallon kafa na garin Kafanchan ya cika makil don kallon wasan karshe na cin Kofin Zaman Lafiya…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce filin wasan kwallon kafa na garin Kafanchan ya cika makil don kallon wasan karshe na cin Kofin Zaman Lafiya da Dan Kwallon Najeriya da ke buga wasa a kasar Norway, Ibrahim Shu’aibu da aka fi sani da Lali ya dauki nauyi. Kungiyar kwallon kafa ta Golden Balley da ke cikin garin Kafanchan ce ta lashe kofin bayan ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Rail Boys da ke Bayan Loko, Kafanchan a bugun finareti.

Dukan kungiyoyin sun nuna bajinta inda suka yi ta kai wa juna hari har aka hura tashi babu wadda ta yi nasarar jefa kwallo a raga, bayan soke kwallon da Balley ta jefa a ragar Bayan Loko da alkalin wasa ya ce an yi satar fage.

A bugun finareti biyar-biyar da aka gudanar na farko dukansu sun zubar da kwallo daidaya inda aka sake bayar da dama ga duk wanda ya zubar an cire shi. Bayan sake bugu na hudu ne ’yan Rail Boys suka zubar da ta karshe ta hannun kwararren dan wasansu yayin da shi kuma mai tsaron gidan Balley ya jefa ta karshe a raga aka tashi da ci 8 – 7.

Kungiyar kwallon kafa ta Takau FC ce ta zamo ta uku bayan ta doke takwararta ta Unguwar Masara da ci 3-0.

An raba kyaututtuka ga kungiyoyi da kuma daidaikun ’yan wasan da suka nuna bajinta a bangarori daban-daban.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci wasan akwai Shugaban Sojojin yankin da wakilin Mai martaba Sarkin Jama’a da Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwar Kafanchan da Sarkin Fawan Jama’a da sauran ’yan kallo maza da mata Musulmi da Kiristoci don kashe kwarkwatan idanu a wasan da aka dade ba a buga irin sa a garin ba.

Yayin da yake mika kyautar kofi ga zakarun gasar, Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Jihar Kaduna (FA), Alhaji Abdullahi Shareeff Kassim ya taya kungiyar murna tare da yin kira a gare su da sauran kungiyoyin da suka fafata a gasar su kara kaimi wajen ganin sun zama fitattu a nan gaba a harkar kwallon kafa, kamar yadda wanda ya shirya gasar a baya ya kasance a wannan filin yana taka leda.

Shugaban ya nuna godiyarsa ga wanda ya dauki nauyin shirya gasar tare da yi masa fatar alheri.

Yayin da yake yi wa manema labarai karin bayani, wanda ya dauki nauyin gasar, Ibrahim Shu’aibu Lali ya nuna godiya ga Allah da Ya ba shi basira da kuma ikon shirya irin wannan gasa don bayar da tasa gudunmawar ta farfado da zaman lafiya da hadin kan da aka sansu da shi a shekarun baya tsakanin Musulmi fa Kirista.

Mutane da dama da Aminiya ta zanta da su a filin sun bayyana jin dadinsu inda suka yi fatan samun wadansu da dama da za su yi koyi da shi.

A wata sabuwa, wani attajiri a yankin mai suna Alhaji Sadiku Shafi’u Tahir (SST) ya shirya gasar kwallon kafar inda ya tattaro kulob-kulob da ke cikin garin Kafanchan da kewaye don fafatawa.

Kungiyar da ta zama zakara an ba ta kyautar kofi da Naira dubu 50 sai ta biyu aka ba ta kyautar Naira dubu 30 yayin da ta uku aka ba ta kyautar Naira dubu 20.