✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gola ya mutu bayan ya yi taho-mu-gama da mai tsaron baya

Wani abu mai kama da almara ya faru a kasar Indonesiya a karshen makon jiya bayan golan kulob din Persela Lamongan mai suna Choirul Huda…

Wani abu mai kama da almara ya faru a kasar Indonesiya a karshen makon jiya bayan golan kulob din Persela Lamongan mai suna Choirul Huda ya rasu bayan sun yi taho-mu-gama da mai tsaron bayan kulob din (defender) Ramon Rodrigues a yayin wani wasa.

Labarin ya nuna a yayin da golan yake kokarin kama kwallo a sama, shi kuwa dan kwallon baya Ramon bai zaci golan ya tashi sama don ya kama kwallon ba, shi ma sai ya tashi don ya fitar da ita da kai al’amarin da ta sa ya zabgawa golan kai a kirji  inda nan take ya zube kasa a sume. Daga nan ne Likitocin da ke kula da ’yan wasan suka garzaya cikin fili don kai masa daukin gaggawa da abin ya ci tura sai aka garzaya da shi asibiti, inda a can ne rai ya yi halinsa bayan lokaci kankane.

dan shekara 38 Choirul ya dade yana yi wa kulob din kwallo, hasalima rahotannin sun nuna ya yi wa kulob din wasanni har sau 500 kuma tun tasowarsa bai taba yin wasa a wani kulob ba, da hakan ta sa mahukunta da kuma takwarorinsa a kulob din suka yi jimamin mutuwarsa a wannan lokaci.

Tuni kulob din ya aika da sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin da kuma Hukumar shirya kwallon kafa ta Indonesiya.