✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a yi jana’izar Farfesa Ali Mazrui

A ranar Litinin da ta gabata ce Allah Ya yi wa fitaccen masanin al’adu da al’amuran al’ummar duniya, Farfesa Ali Al’amin Mazrui rasuwa. Ya rasu…

A ranar Litinin da ta gabata ce Allah Ya yi wa fitaccen masanin al’adu da al’amuran al’ummar duniya, Farfesa Ali Al’amin Mazrui rasuwa. Ya rasu ne a Amurka, bayan jinyar da ya yi ta ’yan watanni. Ya rasu ne yana da shekara 81 a duniya.

Fitaccen malamin, wanda asalinsa dan kasar Kenya ne, ya yi fice a duniya a fagen ilimin al’adun duniya. Haka kuma marubuci ne da ya rubuta littattafai da dama a fagensa na nazari. A 2005, an taba zabensa a matsayin masani na 73 mafi shahara a duniya.
A sakonsa na ta’aziyya, Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ya bayyana marigayin da cewa an yi rashin fitaccen masani a duniya, ba ga Afirika ko kasar Kenya kadai ba.
Marigayi Mazrui ya rasu ne ya bar matan aure guda biyu, daya ’yar Najeriya, dayar kuma ’yar Baturiyar Ingila. Za a dade ana tunawa da shi kan muhimmin aikinsa mai taken Africa: A Triple Heritage, inda ya rika gabatar da gamsassun bayanai na al’adun mutanen Afirika, yadda suka shafi Larabawa, Turawa da kuma Gargajiya.