✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a kammala gasar firimiyar Najeriya

A gobe Asabar 9 ga watan nan da muke ciki ne za a kammala gasar rukuni-rukuni na Najeriya da aka fi sani da NPFL. Dukkan…

A gobe Asabar 9 ga watan nan da muke ciki ne za a kammala gasar rukuni-rukuni na Najeriya da aka fi sani da NPFL. Dukkan wasannin za a yi su ne a lokaci guda watau da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya.

Kulob din Filato United da ke Jos ne yake saman tebur da maki 63 sai kulob din Mountain of Fire Miracle (MFM) da ke Legas yake biye da maki 62 sai Enyimba ke matsayi na uku da maki 58 sai Akwa United da ke matsayi na 4 da maki 57 sai Kano Pillars ke biye da maki 54.

Sannan kulob din Aubakar Bukola Saraki (ABS) da ke Kwara da Gombe United da kuma Remo Stars na Akure ne suka samu koma baya, (relegation) inda suka koma rukunin ’yan dagaji.

Wasannin da za a yi gobe wadanda ake ganin su ne za su fi daukar hankali sun hada da wasan  Filato United  da Enugu Rangers sai wasan Enyimba da Katsina United sai na Akwa United  da Kano Pillars da kuma wasan Elkanemi Warriors na Maiduguri  da kulob din MFM na Legas.

Idan Enugu Rangers ta doke Filato United sannan MFM ta samu nasara a kan El-Kanemi Warriors, to kulob din MFM ne zai zama zakara a gasar inda zai hada maki 65,  amma idan Filato United ce ta samu nasara to babu shakka ita ce za ta zama zakara a gasar ta bana inda za ta hada maki 66 a wasanni 38.

Don haka a yanzu za a iya cewa kallo ya koma sama, inda za a zura ido a ga kulob din da zai lashe gasar ta bana a tsakanin Filato United da kulob din Mountain of Fire Miracle (MFM) na Legas.