✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe ma kin kara

Wani bakauye ne yana waya sai kudi suka kare, sai budurwarsa ta kashe wayarta, idan ya kira sai ya ji an ce masa “not abelabul.”…

Wani bakauye ne yana waya sai kudi suka kare, sai budurwarsa ta kashe wayarta, idan ya kira sai ya ji an ce masa “not abelabul.” Shi kuwa sai ya ce: “Matar nan ba ta barci? To zan kuwa yi maganinta.” Sai ya samu kusa ya rike, ya kira wayar, aka ce masa “not abelabul.” Sai ya soka kusar a wajen ramin sifikar wayar, ya ji ta yi shiru; ya ce: “Gobe ma kin kara!”
Daga Suleiman Abudullahi Zariya 08152402230