✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe Jami’ar Kashere za ta yaye dalibai 1,726

A gobe Asabar ce Jami’ar Tarayya da ke Kashere a Jihar Gombe za ta yaye dalibai 1,726 da suka kammala digiri, inda a cikinsu aka…

A gobe Asabar ce Jami’ar Tarayya da ke Kashere a Jihar Gombe za ta yaye dalibai 1,726 da suka kammala digiri, inda a cikinsu aka samu  50 da suka samu digiri mai daraja ta daya.

A hirara da ’yan jarida, Shugaban Jami’ar Farfesa Alhassan Muhammad Gani ya ce a ranar (gobe) Asabar ce jami’ar za ta gudanar da taron, wanda shi ne yaye dalibanta karo na uku da na hudu da na biyar a hade.

Farfesa Gani ya ce baya ga bikin yaye daliban za su kaddmar da wasu manyan ayyuka da jami’ar ta yi da suka hada da Tsangayar Ilimi da Gwamnan Jihar Inuwa Yahaya zai kaddamar da Babban Dakin Wasanni da Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i zai kaddamar sai kuma Babban Dakin Karatu na Zamani da Ministan Sadarwa Dokta Isa Ali Pantami zai bude.

Sauran ayyukan sun hada da kaddamar da aikin hanya da dasa fulawoyi da sashin Karatun Bai-Daya da Sanata Danjuma Goje zai yi sai Dakin Karatu mai daukar mutum 500 wanda Sakataren Hukumar TetFund Farfesa Suleiman Bogoro zai bude.

Dalibai 629 daga cikin 1,726  sun samu digiri mai daraja ta daya mataki na biyu sai dalibai 873 za su fita da digiri mai daraja ta biyu mataki na biyu sai dalibai 164 masu digiri mai daraja ta uku, sai kuma guda 10 da suka fita da sakamakon tsallake rijiya ta baya.

Farfesa Gani ya ce a lokacin bikin za su bai wa Sanata Muhammad Danjuma Goje da marigayi Dokta Yusufu Bala Usman da marigayi Birgediya Janar Zakariya Maimalari digirin girmamawa.

Daga nan sai ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince a bai wa wasu jami’o’i 12 da aka gina a shekarun 2011 da 2013 wani kason kudi daga Hukumar TetFund wanda Jami’ar Kashere tana ciki kuma za ta kashe kudin ta hanyar gine-gine da suka hada da ofishin Shugaban Jami’a da dakin karatu da kayan aiki na zamani da tuni aka fara.