✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe Barcelona za ta yi wasan sada zumunta saboda A’isha Buhari

Rahotanni sun nuna cewa a gobe Asabar ne kulob din FC Barcelona ta Spain zai kece raini da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a…

Rahotanni sun nuna cewa a gobe Asabar ne kulob din FC Barcelona ta Spain zai kece raini da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a Abuja a wani wasan sada zumunta don karrama matar Shugaban kasa A’isha Buhari a kokarin da take yi na tallafa wa mata da yara marasa galihu.

Wasan, wanda aka yi masa take da “Gumurzu a tsakanin tsofaffin ’yan kwallo” zai kunshi tsofaffin ’yan kwallon kulob din Barcelona ne irin su Edgar Dabis da Samuel Eto’o da sauransu.  A bangaren Super Eagles kuwa, tsofaffin ’yan wasan da za su fafata sun hada da Nwanko Kanu da J.J. Okocha da sauransu.

Za a yi wasan ne a filin wasa na kasa da ke Abuja, kuma ana sa ran manyan mutane daga ciki da wajen kasar nan ne za su kalli yadda wasan zai kaya.

Cibiyar Bunkasa Harkokin Mata ta kasa (National Council for Women Debelopment) da hadin gwiwar Asusun  Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) ne suka dauki nauyin wasan, kamar yadda Darakta Janar ta Cibiyar Harkokin Mata ta kasa, Misis Mary Ekpere-Eta ta sanar wa manema labarai a ranar Litinin da ta gabata.

Ta ce za a kwashe kwana biyu ana gudanar da bukukuwa don jinjina wa matar Shugaban kasa A’isha Buhari a kokarin da cibiyarta ke yi na tallafa wa mata da yara.

A’isha Buhari ta bullo da wani shiri  mai suna Future Assured Programme  da ke koyar da mata musamman mazauna karkara sana’o’in hannu daban-daban da kuma tallafa wa yara marasa galihu.