Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce gobara ta ƙone shaguna 37 a unguwar Zawaciki da ke Karamar Hukumar Kumbotso a jihar Kano.
Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN cewa gobarar ta faru ne da misalin ƙarfe 01:37 na dare wayewar garin yau Laraba.
- Gobara ta yi ta’adi a Kasuwar Idumota da ke Legas
- Gobara ta yi mummunan ta’adi a kasuwar babura a Sakkwato
A cewar Abdullahi, “Mun sami kiran waya da misalin ƙarfe 01:37 na dare daga wani Malam Baba cewa gobara ta tashi a Zawaciki.
“Mun yi gaggawar tattara jami’anmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin ƙarfe 01:47 kuma muka kashe gobarar domin kada ta yaɗu zuwa wasu shaguna,” inji shi.
Abdullahi ya ce, shagunan 37 sun kasance ne a ƙasan bene na wani gini mai shaguna da yawa.
Ya ƙara da cewa, an samu ƙarin wasu shaguna uku da gobarar ta ɗan yi ɓarna.
Kazalika, ya ce ba a samu asarar rai ba, kuma ana kan binciken musabbabin tashin gobarar.