✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta tashi sau 15 cikin kwana 4 a Kano

Wata gobara da ba a san sanadiyyar tashinta ba, ta kama akalla gidaje goma a garin Alharini da ke Karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.…

Wata gobara da ba a san sanadiyyar tashinta ba, ta kama akalla gidaje goma a garin Alharini da ke Karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.

Wutar wacce ta fara tashi a ranar Alhamis din makon jiya ta kai tsawon kwana hudu tana tashi a lokuta daban-daban inda aka samu asarar ma’ajiyar hatsi da dabbobi da suka hada da sa da raguna 3 da awaki 11.

Malam Muhammad Sanusi Dalhatu shi ne Dagacin Alharini ya shaida wa Aminiya cewa tashin wutar ya zama wani abu na mamaki a yankin lura da yadda wutar ta rika kamawa a gidaje daban-daban wadanda ba su makwabtaka da juna a kuma mabambantan lokuta.

“Wutar ta fara tashi ne da misalin karfe 10 na safe a kofar gidan wani mutum mai suna Malam Yusha’u lokacin da ake kokarin kashe ta sai kuma ta kama a wani gida da ke nesa da shi. Bayan wani lokaci kuma sai ta sake tashi a wani gida a nesa da wancan. To a wannan ranar kadai sai da wutar ta tashi sau 10. Abin mamakin a tashin wutar shi ne yadda wutar ta rika tashi a gidaje daban-daban da ba makwabtan juna ba. Washegari ranar Juma’a sai ta tashi sau biyu, haka ranar Asabar ta tashi sau biyu a ranar Lahadi kuma ta tashi sau daya,” inji shi.

Da aka tamabaye shi game da matakin da suka dauka wajen kashe gobarar Dagacin ya ce sun kira jami’an kwana-kwanan inda suka zo a kan lokaci suka kashe wutar, “Amma daga baya mu muka ci gaba da kokarin kashe wutar har zuwa kwanakin da wutar ta ci gaba da tashi. Mu dai mun dauki matakin yin addu’ar neman tsari daga wutar da kuma kara aukuwarta a nan gaba,” inji shi.

Malam Yusha’u Shu’aibu daya ne daga cikin wadanda bala’in gobarar ya shafa ya ce lokaicn da abin ya faru ba ya gida sai kiransa aka yi aka sanar da shi. “Kafin in zo gidan wutar ta ci abin da za ta ci dakunana sun kone na yi asarar dabbobi,” inji shi.

Shi ma Malam Kabiru da gobarar ta shafa inda ya rasa dabbobi da dakunansa, ya yi kira ga gwamnati ta tallafa musu don rage radadin abin da suka rasa a sanadiyyar tashin wutar.

Sa’idu Muhammad shi ne Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin inda ya ce jami’ansu sun kai daukin gagagwa a lokacin da wutar ta fara tashi a ranar Alhamis inda aka yi nasarar kashe wutar a dukkan wuraren da ta tashi.

Sai dai ya ce har zuwa yanzu ba su gano dalilin tashin wutar ba.