✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a gidan Akanta-Janar na Jigawa

A ranar Talatar da ta gabata ce gobara ta tashi a gidan Akanta-Janar na Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Aminu. Wakilinmu wanda ya ziyarci gidan, ya…

A ranar Talatar da ta gabata ce gobara ta tashi a gidan Akanta-Janar na Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Aminu.

Wakilinmu wanda ya ziyarci gidan, ya ga yadda gobarar ta yi barna inda ta lashe dukiya ta miliyoyin Naira.  Sai dai ba a samu labarin asarar rai a yayin gobarar ba.

Rahotanni sun ce ba a san dalilin tashin gobarar ba, amma wadansu suna zargin wutar ta tashi ne lokacin da aka dawo da wutar lantarki inda wadansu daga cikin wayoyin wutar lantarki na gidan suka hadu kafin su kama da wuta.

Wata majiya ta ce, abin takaici ne ganin yadda gobarar ta shafe awanni kafin a shawo kanta, inda ta rika cin kowane sashe na gidan kafin jami’an kwana-kwanan da makwabta da  sauran jama’a da suka kai dauki su shawo kanta.

Wani mazaunin gidan Malam Nasiru da wakilinmu ya zanta da shi ya ce da misalin karfe 12 na rana ne  lokacin da aka kawo wutar lantarki sai ya canja layin daga janareta. Ya ce ba a dade ba sai ya ji wadansu na kururuwar wuta ta tashi. Daga nan ne ta rika ci kuma ana ganin ta fara ne daga dakin maigidan Alhaji Ahmed Aminu wanda yake Saudiyya lokacin da lamarin ya faru. Daga nan ne ta watsu zuwa sassan gidan, kuma kafin ma’aikatan kwana-kwana su iso ta yi barna.

Majiyarmu ta ce lokacin da gobarar ta faru uwargidan Akantan da ’ya’yansu da sauran ma’aikatan gida suna ciki.

Zuwa hada wannan rahoto wakilinmu bai samu damar jin ta bakin Akanta-Janar din ko uwargidansa game da faruwar lamarin ba.