✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta sake lakume dukiya a kasuwar Balogun a Legas

Da safiyar yau Laraba ne gobara ta sake tashi a kasuwar Balogun da ke cikin garin Legas. Wani da yake kasuwancinsa a daura da wajen…

Da safiyar yau Laraba ne gobara ta sake tashi a kasuwar Balogun da ke cikin garin Legas.

Wani da yake kasuwancinsa a daura da wajen da wutar ta tashi Malam Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa gidan da wutar ta kama da ake kira Anambra Falaza a baya gidan ya taba yin gobara, a lokacin da ta kama ‘yan kasar China ne ke kasuwancin bada sari a gidan.

Ya ce gobarar a wannan karon ta taɓa gidaje da shagunan da ke daura da gidan, ” Yanzu haka ‘yan kasuwa da ke daura da gidan na kokarin kwashe kayayyakinsu a lokacin da jami’an kashe gobara ke kokarin shawo kan lamarin.”

Gobarar ta tashi a kasuwar Balogun cikin kasa da kwanaki biyar da gobara ta tashi a kasuwar katako ta Amu da ke Mushin duk a jihar ta Legas.

A garin Shagamun jihar Ogun ma gobarar ta tashi a kasuwar Sabo Shagamu, kasuwa mafi tsufa ta Hausawa da ake hada-hadar goro, da kayan abinci da suka hadar da wake da kuma sutura irin su shaddodi da atamfofi.

A cewar Maikanuri na Jihar Ogun Alhaji Muhammadu Gana, wanda fadar ce daura da kasuwar gobarar ita ce, irin ta na biyu tun bayan da Basaraken Yarbawa yankin ya basu kasuwar, ” An taba samun irin wannan gobara shekaru 25 da suka shude a lokacin mulkin Janar Abacha, amma wannan lokacin lamarin bai yi kyamari tamkar na jiya ba, domin an yi asarar dukiya sosai muna jajantawa jama’a baki daya da fatan Allah ya kiyaye na gaba”

Gwaman jihar Ogun Dapo Abiyodun, ya kai wa ‘yan kasuwar ziyarar jaje a safiyar yau ya kuma ganewa idanunsa barnar da gobarar tayi.