✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta sa an rufe sashen Majalisar Tarayya

Lamarin ya faru da yammacin ranar Alhamis.

Takardu da kayan ofis da dama sun kone kurmus bayan wata gobara da ta tashi a Majalisar Tarayya.

A cewar sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Majalisar, Emmanuel Agada, ya fitar a ranar Alhamis, gobarar ta tashi ne a daki mai lamba 227 a sabon reshen majalisar wakilai da misalin karfe 6 na yamma.

Mista Agada ya ce ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon matsalar wutar lantarki, amma hadin kan ma’aikata da jami’an hukumar kashe gobara sun taimaka wajen takaita yaduwar wutar.

“An kashe gobarar tare da taimakon ma’aikatan da ke bakin aiki, inda nan take suka kutsa cikin ofishin da abin ya shafa don kashe wutar kafin isowar jami’an kashe gobara,” in ji sanarwar.

Sai dai ya ce lamarin na iya shafar ’yan majalisa da ma’aikatan da ke amfani da wannan sashe na wani lokaci.

“Ana sa ran bayan tantancewar da hukumar kashe gobara da hukumar kula da gidaje da ayyuka suka yi, za a ci gaba da aiki a wannan sashe, gidaje da dukkan manyan jami’an majalisar wakilai da na ma’aikatu, nan take,”

A yanzu haka dai ana gudanar da wani gagarumin gyara a harabar Majalisar Dokoki ta Kasa, musamman bangaren ‘White House’ da ke da Majalisar Dattawa da ta Wakilan da wasu ofisoshi.

Ko da yake a halin yanzu ’yan majalisar na hutun shekara har zuwa watan Satumba, wasu kwamitoci na ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Ba a dai sani ba ko wannan gobarar za ta iya shafar wadannan kwamitocin da ke aiki ba.