✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta ci dakin ajiye gawa ta kone gawarwaki 12 a Osun

A yau Talata gobara ta ci dakin ajiye gawa na jami’ar Obafemi Awolowo University (OAU) Ile-Ife, jihar Osun. Gobarar ta kone gawarwaki 12 cikin gawarwaki…

A yau Talata gobara ta ci dakin ajiye gawa na jami’ar Obafemi Awolowo University (OAU) Ile-Ife, jihar Osun. Gobarar ta kone gawarwaki 12 cikin gawarwaki 102 da ke ajiye a dakin.

Jami’in hulda da jama’a na jami’ar Mista Abiodun Olarewaju, ne ya sanar da hakan, ya kuma ce hukumar jami’ar duk ta yi shiryeshirye ga masu ajiye gawa a dakin saboda gudun irin wannan iftila’in.

Gobarar ta tashi ne a tsangayar ilimin jikin mutum, Hukumar kashe gobara ta jami’ar ce tayi nasarar kashe gobarar, wanda ta tashi da misalin karfe 3:00 na tsakar dare sanadiyyar wutar lantarki.