✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta ƙone shaguna 37 a Kano

Gobara ta ƙone shaguna 37 a unguwar Zawaciki da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce gobara ta ƙone shaguna 37 a unguwar Zawaciki da ke Karamar Hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN cewa gobarar ta faru ne da misalin ƙarfe 01:37 na dare wayewar garin yau Laraba.

A cewar Abdullahi, “Mun sami kiran waya da misalin ƙarfe 01:37 na dare daga wani Malam Baba cewa gobara ta tashi a Zawaciki.

“Mun yi gaggawar tattara jami’anmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin ƙarfe 01:47 kuma muka kashe gobarar domin kada ta yaɗu zuwa wasu shaguna,” inji shi.

Abdullahi ya ce, shagunan 37 sun kasance ne a ƙasan bene na wani gini mai shaguna da yawa.

Ya ƙara da cewa, an samu ƙarin wasu shaguna uku da gobarar ta ɗan yi ɓarna.

Kazalika, ya ce ba a samu asarar rai ba, kuma ana kan binciken musabbabin tashin gobarar.