Wata gobara da ta tashi a cikin wani kwala-kwalen ‘yan ci rani a tsakiyar teku ta hallaka mutane tare da kifar da jirgin a bakin gabar Libya.
Tashin gobarar da kuma kifewar jirgin ya faru ne a bakin gabar Sabratha da ke Yammacin Libya.
- ’Yan ci-rani 12 sun daskare a dusar kankara a kokarinsu na shiga Turai
- An ceto ’yan ci-rani 150 da jirgin ruwa ya kife da su a gabar Spain
Wani Kakakin Kungiyar Agaji ta Red Crescent a kasar Libya, Tawfik Al Shuklri ne ya bayyana haka a karshen makon nan, a cewar TRT.
Kakakin ya kuma bayyana cewa, wasu jami’an gwamnati ne su ka sanar da su ganin wasu gawarwaki da igiyar ruwan teku ta watso su bakin gaba.
Sannan ya ce, kungiyar agajin ta kwashe gawarwakin ta kuma kai su asibiti a inda za a cigba da gudanar da binciken musabbabin mutawar su.
A wani hoton bidiyo da ya karade shafukan intanet ya nuna wani bangare na jirgin ruwan da ya kone da tare da wasu gawarwaki makale a jikinsa.
Galibi dai ana samun rahoton yadda ‘yan ci rani daga Afirka ke ratsawa ta kasar Libya a kokarin tsallakawa kasashen Turai ta Bahar Maliya.