✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Giwa ta murkushe wani dan Saudiyya a Uganda

Garken giwayen ya balle sannan ya yi tafiyar ruwa da mutumin da ya je yin fitsari.

Giwaye sun murkushe wani mutum dan asalin kasar Saudiyya har lahira a lokacin da yake yawon bude ido a wani gandun daji a kasar Uganda.

Mutumin yana yawon bude idon ne tare da abokansa a mota cikin gandun dajin ‘Murchison Falls National Park’ ne lokacin da ajali ya kira shi.

Ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da garken wasu giwaye suka balle suka yi kansa gaba-gadi, suka yi tafiyar ruwa da shi.

Masu yawon bude idon suna hanyarsu ta zuwa birnin Arua da dare ne suka fita daga motarsu domin biyan bukata da dare, a nan ne shi kuma ya gamu da ajalinsa.

Lamarin ya faru a daren ranar Talata, amma hukumomin da ke aiki da gandun dajin ba su ga gawar mutumin ba sai zuwa safiyar ranar Laraba.

Hukumomin da ke kula da gandun sun tabbatar da aukuwar lamarin kuma sun ce ana gudanar da bincike a kai.

Farmakin da dabobbi suke kai wa masu yawon bude ido a kasar Uganda ya zama ruwan dare.