Barkanmu da warhaka Manyan gobe. Tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Giwa da Kunkuru’. Labarin na nuni da yadda karshen munafunci yake kasancewa. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Akwai wani daji da Sarkinsu Giwa ce. ita Giwa tana da girma da kuma karfi don haka sai suka nada ta Sarki. Abin ya yi matukar batawa Kunkuru ra don a nasa tunanin, shi ya fi Giwa wayo da dabara.
Ran nan dabbobin dajin suka rasa abin da za su ci sai aka je wajen Giwa. Giwa ta nemi a ba da shawara akan mafita. Nan take Kunkuru ya ce a shanye kwan tsuntsaye,duk da yake abin bai yi wa tsuntsayen dadi ba haka ake ta shanye kwansu har suka yi laushi saboda tsabagen yin kwai.
Duk da wannan dabarar dabbobin ba su daina jin yunwa ba. Sai Kunkuru ya sake bada shawarar cewa a cinye kifayen dake cikin ruwa. Da farko abin bai yi wa sauran dabbobin dadi ba sai da Kunkuru yace “ai su a ruwa suke rayuwarsu kuma ba za su iya wata rayu ba a kan kasa ba don haka su ba dabbobi bane”.
Sauran dabbobin ba su yi wata-wata ba suka shiga kama kifaye har sai da suka cinye kifayen kaf amma duk da haka ba su koshi ba.
Sarki ta sake neman shawarar Kunkuru akan abin yi. A nan ne Kunkuru ya ce yana da shawara amma sai in Sarki zai masa alkawarin mayar da shi mataimakinsa. Abin bai yi wa Sarkin dadi ba amma da ta ga yadda sauran dabbobin ke murna sai ta yi na’am da shawarar.
Kunkuru ya je ya sami maciji ya ce ya taimake sa ya fada wa dabbobin cewa shi ya fi cancanta ya zama Sarki ba Giwa ba. Maciji da yake ya san halin Kunkuru sai ya ki.
Washe gari maciji ya fada wa Sarki abin da Kunkuru ke shirya mata. Sarki ta sa aka kamo Kunkuru aka kashe.
Manyan gobe kun yi yadda karshen munafuki Kunkuru ta kare, saboda haka sai ku yi hattara.