✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Girkin dankalin Turawa a cikin kwai

Sallama a gare ki uwargida, tare da fatan alheri kuma ana lafiya. Yaya sanyi? Allah Ya fid da mu lafiya amin. A yau na kawo…

Sallama a gare ki uwargida, tare da fatan alheri kuma ana lafiya. Yaya sanyi? Allah Ya fid da mu lafiya amin. A yau na kawo muku yadda ake girka dankalin Turawa a cikin kwai. Akwai hadi da dama wanda ake yi da dankalin Turawa. Don haka na kawo muku irin wannan hadin, tare da fatan za a amfana da shi kuma wata rana za a gwada yi wa maigida ko yara. A sha karatu lafiya.

Abubuwan da za a bukata
•Dankalin Turawa
• Man gyada
•kwai
•Albasa
•Tumatir
•Magi

Hadi
Da farko dai za a fere dankalin Turawa sannan a yayyanka shi kamar za a soya. A wanke a zuba gishiri kadan sannan a dora man gyada a wuta, sai a zuba har sai ya soyu, sai a kwashe.
A yayyanka tumatir da albasa kanana sannan a fasa kwai kamar shida, sai a zuba a ciki da magi da gishiri kadan sannan a kwaba su sosai.
A rage man tuya zuwa kadan sannan a zuba kwai, sannan a debo soyayyen dankalin Turawar a zuba a kai. Idan ya dan soyu, sai a kwashe da cokali sannan a sake zuba wani hadin kwan a tukunyar suyar, sannan sai a juya ta gefen dankalin da bai samu kwan ba. A zuba a cikin kwan har sai sun soyu. Haka za a rika yi har sai an gama.
Za a iya cin wannan girkin da safe a matsayin abin karyawa tare da shayi.