✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gini mai hawa uku ya rusa, ya kashe mutum bakwai

Gini mai hawa 3 ya rusa a kan titin Herbert Macaulay  da ke gefen Layin Oloto a unguwar Ebutte Metta da ke birnin Ikko ya…

 Farfajiyar da ginin ya rusaGini mai hawa 3 ya rusa a kan titin Herbert Macaulay  da ke gefen Layin Oloto a unguwar Ebutte Metta da ke birnin Ikko ya kashe mutum bakwai. Yayin da ya rubza, an zaro mutum hudu matattu, kamar yadda wadanda  ke cikin  gidan suka yi bayani.  

Sun ce ginin ya fara ba da alamar  rushewa tun wani lokaci can baya, kuma a wannan karo sai da ya fara zubar da kasa alamar cewa zai rusa,  wasu daga  cikin  mutanen da ke cikin gidan har sun fita, amma bayan awoyi bai rusa ba, sai suka koma. Abin kaddara, komawarsu ke da wuya, sai ya rusa, inda nan take aka zaro mutum hudu matattu, wasu kuma da rai.
Wani makwabcin gidan mai suna Ade Kusheru ya shaida wa Aminiya cewa ya ji karar rushewar ginin, bayan ya fita sai ya yi kicibis da daya daga cikin mutanen gidan yana kuwwar  matarsa  da ’ya’yansa duk suna ciki. “Wasu makwabta suka yi kunar-bakin-wake cikin ginin, suka fito da su. Haka nan sun dauko wata mata, wadda kanta ya rabu da gangar jikinta. Sannan an samu wani yaro mai kimanin shekara guda da rai.” Inji shi.
Mai magana da yawun hukumar ba da  agajin gaggawa,  Mista Ibrahim Fariyola ya shaida wa Aminiya cewa labarin rushewar  ginin ya je musu cikin dare, rashin cunkoson motoci ya jaza isarsu wurin cikin lokaci suka  fara aikin ceto, kuma suka kira sauran hukumomin da ke da nasaba da aikin ceto suka kama aiki gadan-gadan.
Bincike ya nuna cewa an  gina  gidan sama da shekaru 40 da suka shige.