✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gine-ginen Kasuwar Barci sun fara isa kasa

Gwamnatin Jihar Kaduna ta samu nasarar fara aiki a Kasuwar Barci kwana uku bayan wa’adin da Hukumar Raya Birnin Kaduna (KASUPDA) ta ba ’yan kasuwar…

Gwamnatin Jihar Kaduna ta samu nasarar fara aiki a Kasuwar Barci kwana uku bayan wa’adin da Hukumar Raya Birnin Kaduna (KASUPDA) ta ba ’yan kasuwar na su fice daga cikinta.

A ranar Juma’a makon jiya da daddare ne Hukumar KASUPDA ta lillika takardun ba ’yan kasuwar wa’adin kwana uku da su kwashe kayansu domin za ta fara aikin sabunta kasuwar. A cewar Hukumar KASUPDA umarnin ya zama dole saboda shirin sabunta garin Kaduna da gwamnatin jihar a karkashin Malam  Nasir El-Rufa’i ke aiwatarwa. Ta nemi ’yan kasuwar su bar kasuwar kafin a zo rusa ta domin sake ginata ta zama ta zamani.  Wakilinmu wanda ya ziyarci kasuwar ya gano cewa ’yan kasuwar sun wayi garin Asabar cikin alhini sakamakon ganin wadannan takardu na wa’adi like a shagunansu.

Gwamnan Jihar ya sha nanata alwashin gyara tare da sabunta manyan kasuwannin jihar kuma tuni an tada wasu kasuwannin jihar ciki har Kasuwar Kawo Kaduna da ta Sabon Gari da ta Dan Magaji duk a Zariya domin sabunta su.

Wani dan gwanjo  da ya ce sunansa Shehu ya ce sun wayi gari ne kawai a ranar Asabar da safe suka ga an lika musu takardar wa’adin kwana uku. “Gaskiya hankali ya tashi domin babu yadda za a yi jama’a su kammala kwashe kayayyakinsu cikin kwana uku ba tare da sanin inda za mu kai kayayyakinmu ba,” inji shi.

Shi ma Abubakar da ke sana’ar dinki a kasuwar ya ce tuni suka kwashe kayayyakinsu zuwa wani shago da suka kama kusa da kasuwar. “Mu kusan hudu ne a shagon kuma mu uku muna da aure da ’ya’ya, amma aka tarwatsa mu cikin ’yan kwanaki. Yanzu haka mun dan roki wani mutum ne da ya ba mu hayar shago na wata uku kafin mu samu wani wurin. Amma fa akwai da yawa da ba su san inda za su saka kansu ba, ballantana kayansu,” inji shi.

Ustaz Aminu wanda ke sayar da kaftani ya koka da yadda ya ga jama’a na kwashe kayayyakinsu ba tare da sanin inda za su kai ba. “Ina laifin a fara aikin kashi-kashi, maimakon a tada mutane dubbai cikin ’yan kwanaki. Gyara abu ne mai kyau amma yadda aka ba mu umarnin tashi cikin kwana uku gaskiya babu tausayin talaka a ciki,” inji shi Ya ce a shagunsu kusan su 10 ne ke cin abinci ban da yara da ke zuwa koyon sana’a domin dogaro da kansu.

Shi ma Sani Tela cewa ya yi, “Kwanan nan na sabunta biyan kudin hayar shekara na shagonmu, sai gashi an ce duk mu tashi. Yanzu haka inda za mu kai kayayyakinmu ajiya ba mu da shi, dole sai dai in kai gidanmu,” inji shi.

Malam Dahiru DD Guy, mai gwamnjo ya ce Kasuwar Barci dai ta tarwatse domin mafi yawan ’yan kasuwar duk sun kwashe kayayyakinsu sun fice domin kuwa tuni wa’adin da aka ba su ya kare a daren Litinin da ta gabata.

Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwar, Alhaji Haruna Dabai wanda ya tabbatar wa  wakilinmu halin da ’yan kasuwar suka tsinci kansu, ya ce sun wayi garin Asabar ce kawai suka ga wa’adin kwana uku.

“Mun gana da Hukumar Raya Kasuwar da kuma ita kanta Hukumar KASUPDA kan yadda za a duba a ba mu damar fitowa da matsayi ko tsarin da zai rage damuwar ’yan kasuwarmu. Cikin hukuncin Allah sun yarda mun zauna da su kan yadda za a daidaita kuma sun amince mu zauna mu ga me muke so a yi, wanda idan sun ga ya yi daidai da tsarin za su yarda. In bai yi ba, ba za su yarda ba,” inji shi.

Kakakin Hukumar KASUPDA Nuhu Garba Dan’ayamaka ya tabbatar wa  Aminiya cewa hukumar ta samu ganawa da kungiyar ’yan kasuwar. Ya ce batun rusa kasuwa ba ’yan Kasuwar Barci kadai ya shafa ba, domin an yi irin haka a Kasuwar  Sabon Garin Zariya da ta Dan Magaji, a cewarsa ci gaba ne ya zo wa jihar kuma zai amfani jama’a.

Ya nemi ’yan kasuwar su ci gaba da hakuri a yayin da suka kwashe kayansu. Sannan ya nanata cewa kafin nan hukumar ta ba ’yan kasuwar takardar wa’adi na mako uku, amma wadansu ba su tashi ba har sai da aka aike musu da wa’adi na biyu.

Game da ko akwai shirin ba su wani wuri sai ya ce hukumar tana ci gaba da duba bukatunsu a tattaunawa da suke yi.

Gini ya kashe wani matashi

A shekaranjiya Laraba kuma wani matashi ya rasa ransa a lokacin da gini ya fado masa tare da wadansu abokansa a kasuwar.

Daya daga cikin matasan wanda aka fi sani da Daddy shi ma ya samu mummunan rauni.

Aminiya ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne da misalin karfi 3:40 na rana lokacin da matasan ke cire karafa da wayoyin wutar lantarki a shagunan da aka rusa a kasuwar.