✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sarkin Zazzau: Gidajen sarauta sun yi mubaya’a

Gidajen Barebare, Katsina, Malamai da wakilan unguwanni sun yi mubaya'a ga Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli

Gidan sarautan Barebare da na Katsinawa a Masarautar Zazzau sun yi mubaya’a ga sabon Sarki Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli.

Yariman Zazzau, Alhaji Munnir Ja’afaru ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai bayan gaisuwar da gidajen suka kai wa sarkin a ranar Alhamis.

Gidan Katsinawa sun yi wa sarki mubaya’a ne karkashin jagorancin Wamban Zazzau Alhaji Abdulkarim Amin, iyalan marigayi Sarki Shehu Idris.

Sauran wadanda suka yi mubaya’ar sun hada da wakilai daga Gidan Barebari, Gidan Mallawa da Gidan Malamai sai kuma wakilan unguwanni.

Tun da farko sarkin ya yi alkawarin aiki da tare gidajen sarautar masarautar sannan ya kirayi jama’arsa su hada kai su zauna lafiya.

A jawabinsa bayan sanar da nada shi, Sarki Ahmed ya ce zai yi dukkan mai yiwuwa wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a masarautar domin samar da cigaba.

“Akwai kyakkyawar dangantaka tsakanina da sauran gidajen Saurautar Zazzau kuma mun gaji girmama juna a matsayin ’yan uwa na jini”, inji sarkin a yayin bayyana kusancinsa da sauran gidajen saurautar masarauta na Katsinawa da Barebari a masarautar.

 

%d bloggers like this: