daukacin gidajen kallon kwallo da ke birnin Jos sun ce sun dauki matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyin al’umma a wajen nuna gasar a kokarin da suke na kaucewa hare-haren bam da ake kai wa gidajen kallon kwallo a birnin.
Kamar yadda wakilinmu ya kalato a wata hira da gidan rediyon Deutsche Welle (DW) na Jamus ya yi da Shugaban masu gidajen nuna kwallo na Jihar Alhaji Zakari Muhaammad a shekaranjiya Laraba ya ce tuni kungiyarsu ta yi tarurruka da jami’an tsaro a kan yunkurin daukar matakan tsaro a yayin gasar.
Shugaban ya ce daga cikin matakan tsaron da kungiyarsu ta dauka sun hada da rashin nuna wasannin da za a yi su cikin dare. Gidajen kallon za su nuna wasannin da za a yi su ne kawai da rana ko da yamma watau ido-na-ganin ido. Sannan ya shawarci gidajen kallo da su tabbatar masu ababen hawa sun ajiye su nesa da gidajen kallo kuma a karkashin kulawa ta musamman.
Ya ce da yawa daga cikin ’ya’yan kungiyarsa sun yanke shawarar kin nuna gasar saboda tsoron da suke ji na abubuwan da ke iya faruwa amma wasu kuwa sun sha alwashin nuna gasar ba tare da shakkar komai ba.
“Wasu daga cikin ’ya’yan kungiyarmu sun ce ba za su nuna gasar ba amma wasu sun tabbatar za su nuna bayan sun dauki matakan tsaro”, inji shi.
A birnin Tarayya Abuja kuwa, Ministan Babban Birnin Tarayya Sanata Bala Muhammad ya shawarci gidajen kallon kwallo da su hakura da nuna gasar a lokacin gasar cin kofin duniya saboda yiwuwar kare-hare a gidajen kallon kwallon.
Ministan ya ce saboda matsalar tsaro yana shawartar jama’a da su zauna a gidajensu su kalla ba lallai sai sun halarci gidajen kallon kwallon ba.
Idan za a tuna a kwanakin baya ne dai wasu mahara suka kai harin bama-bamai a wasu gidajen kallon kwallo a garuruwan Jos da Maiduguri inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa.
…Gidajen kallon kwallo sun dauki matakan tsaro don nuna gasar a Jos
daukacin gidajen kallon kwallo da ke birnin Jos sun ce sun dauki matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyin al’umma a wajen nuna…