✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Olamfik: ’Yar Saudiyya ta ki yarda ta fafata da ’yar Isra’ila a wasan Judo

Wata yarinya ’yar Saudiyya da ke wakiltar kasar a gasar wasanni ta Olamfik da take gudana a yanzu haka a Brazil a bangaren wasan Judo…

Wata yarinya ’yar Saudiyya da ke wakiltar kasar a gasar wasanni ta Olamfik da take gudana a yanzu haka a Brazil a bangaren wasan Judo na mata Joud Fahmy ta ki amincewa ta fafata da takwararta da ta fito daga Isra’ila a wasan.
An shirya fafatawar ce a tsakanin Joud Fahmy da kuma ’yar Isra’ila Christainne Legentil a wasan Judo zagayen farko amma da Fahmy ta lura za ta kara ne da ’yar Isra’ila sai ta yi karyar ba ta da lafiya, inda ta ce ta ji rauni a yayin atisaye a hannunta da kuma a kafarta da hakan ba zai ba ta damar yin wasan ba.
Sai dai jim kadan bayan hakan ta faru ne sai wasu kafofin watsa labarai suka gano cewa Joud Fahmy ’yar  shekara 22 ba ta samu wani rauni ba, ta yi haka ne kawai da gangan don gudun ka da ta hadu da ’yar kasar Isra’ila a wasan.
Kamar yadda wani gidan Talabijin na Isra’ila mai suna Times of Isreal, Channel 2 ya ruwaito, ya ce ’yar Saudiyyar ta yi haka ne don gudun kada ta hadu da ’yar kasarsu a wasan zagayen farko na Judo a gasar ta Olamfik.
Ita dai Joud Fahmy tana daya daga cikin ’yan wasa hudu da kasar Saudiyya ta amince su halarci gasar Olamfik da yanzu haka ke gudana a Brazil.
A shekarar 2012 ce kasar ta fara halartar gasar Olamfik da ta gudana a Landan a karon farko, inda ta tura ’yan wasa biyu kacal don haka za a iya cewa yanzu an samu cigaba ne bayan ta tura ’yan wasa hudu mata.
Dangantaka a tsakanin Saudiyya da Isra’ila dai ta yi tsami inda yanzu haka ba sa ga-maciji da juna.  Hasalima Saudiyya ba ta amince ’yan kasarta su kai ziyara ko yin hulda da Isra’ila ba.  Wannan ne ya sa ake hasashen ’yar wasan Judo Joud Fahmy ta ki fafatawa da ’yar Isra’ila Christiannne Legentil ce saboda wannan matsala.